An takaita sadaki a Jamhuriyar Nijar

An kafa dokoki domin saukaka wa mutane aure a Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kafa dokoki domin saukaka wa mutane aure a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, masarautar Damagaram ta bi sahun takwararta ta Azbin tare da amincewar al'ummar yankin ta kafa wasu dokoki domin saukaka aure, wadanda suka hada da kayyade kudin sadaki, da hana anko da takaita gara da kuma jerin gwanon ababan hawa ana wasan ganganci wajen kai amarya.

Haka kuma masarautar ta Damagaram, ta hana shan tabar nan ta ruwa wato shisha da matasa ke yi a fadin jihar.

Sarkin garin mai martaba Alh. Abubakar Sanda, ya sanar da hakan a yayin wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki a jihar da 'yan kasuwa da kuma kungiyoyin mata, inda ya ce an dauki wannan mataki ne bayan jama'ar garin sun kai kukansu ga masarautar, a kan a nema musu sauki a al'amuran da suka shafi aure da suna da kuma wasu bidi'oi da ake yi a jihar.

Mai martaba sarkin na Damagaram, ya ce sun yi nazari a kan wannan koke, don haka yanzu aka sanya doka saboda la'akari da cewa dukkan wadannan abubuwa da jama'ar garin suka mayar bidi'a, abubuwane da addini ya hana su.

Kazalika mai martaba sarkin ya ce, irin wadannan bidi'ar, kan sa idan ta zo kan mutum, wani lokaci sai an ci bashi domin a yi abin da zai faranta wa jama'a.

Yanzu haka, masarautar ta Damagaram ta kayyade sadakin aure daga jaka 20 na CFA zuwa jaka 50, kuma an hana kai amarya a cikin jerin gwanon motoci, sannan an takaita gara da ma hana ankon biki kwata-kwata.

A bangaren lafiya kuma, masarautar ta Damagaram, ta hana shan tabar shisha kwata-kwata bisa shawarwarin likitoci, saboda a cewar masarautar, likitoci sun ce yawanci matasa na kamuwa da cutukan da suka danganci huhu ko tari sakamakon shan shishar.

Matasan garin dai sun bayyana jin dadinsu ga wadannan sabbin dokoki, musamman dokar takaita kashe kudade a yayin aure,inda suka ce da yawa daga cikinsu na son suyi aure, to amma idan suka tuna irin kudin da za su kashe, jikinsu kanyi sanyi.

Masarautar Azbin ma dai a Jamhuriyar ta Nijar, ta dauki irin wannan mataki na hana bidi'a ya yin biki ko suna.

A baya dai, wata karamar hukuma a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta so daukar irin wannan mataki amma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya hana ta.

Labarai masu alaka