An soma shirin tsige shugaban kasar Zambia

Edgar Lungu.

Asalin hoton, AFP

Mambobin jam'iyyar hamayya ta Zambia sun gabatar da wani kudurin doka a zauren majalisar da zummar tsige shugaban kasar Edgar Lungu.

Kusan kashi uku cikin hudu na 'yan majalisar karkashin jam'iyyar United Party for National Development ne suka sanya hannu kan kudurin dokar, wanda aka gabatar a gaban majalisar ranar Alhamis.

Wasu daga cikin mutanen da suka sanya hannu kan kudurin sun hada da tsofaffin ministoci Chishimba Kambwili da Harry Kalaba, wadanda mambobin jam'iyya mai mulki ne.

'Yan majalisar sun ce sun dauki matakin ne saboda rashin iya aiki da kuma cin hanci da suke zargin shugaban kasar da aikatawa.

Sai dai kakakin shugaban ya yi watsi da zarge-zargen.

Tuni harkokin siyasar Zambia suka dauki dumi duk da yake ba za a yi zaben shugaban kasa ba sai 2021.