Buhari ya gana da dalibai 107 da aka sako

'Yan matan sakadaren Dapchi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya yi alkawali ceto sauran 'yan Matan Chibok

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi su fiye da 100 a fadarsa da ke Abuja.

An gabatar wa shugaban 'yan matan ne bayan da aka bincike lafiyarsu tare da kwantar musu da hankali.

A jawabinsa lokacin ganawar, Shugaba Buhari ya ce "Ina farin cikin sanar da 'yan Najeriya da abokanmu na kasashen waje da kuma wadanda muke hada gwiwa da su cewa an sake su ne ba tare da sharadi ba.

Dalibai 107 ne dai aka sako kuma 105 daga cikinsu 'yan matan makarantar Dapchi ne da kuma mutum biyu da Boko Haram ta sace.

Shugaban ya ce sakin matan, bayan da ya umarci jami'an tsaron kasar su tabbatar babu abin da ya same su, "abin farin ciki ne."

"Na umarci dukkan jami'an tsaro da su yi aiki domin tabbatar da cewa ba mu sake ganin irin wannan lamarin ba" a cewar shugaban.

Sannan ya yi gargadi ga shugabannin hukumomin tsaro cewa da kada su kuskura a sake samun wani cikas daga bangarensu, yana mai cewa "ba zan dauki hakan da wasa ba."

Ya kuma tabbatar wa da daliban da aka kubutar cewa za su rayuwa cikin 'yanci da cimma burinsu na rayuwa a Najeriya cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tsoron wani tashin hankali ko cin zarafi ba.

Shugaba Buhari kuma ya sha alwashin ganin an sako daliba daya da ta rage a hannun mayakan Boko Haram da kuma 'yan matan Chibok da aka sace tun 2014

Ranar Laraba aka sako 'yan matan, wadanda aka sace a watan jiya

Mahaifin daya daga cikin 'yan matan, Kundili Bukar, ya gaya wa BBC cewa wasu mutane da ake tsammani 'yan Boko Haram ne suka mayar da matan a motoci.

Abin da ya faru tun sace 'yan Matan

Hakkin mallakar hoto GGSS
 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace 'yan matan
 • Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
 • Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce

A cewarsa, sun ajiye su ne kawai suka tafi kuma 'yan matan sun nuna alamar matukar gajiya.

Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi zargin cewa jam'iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan domin cimma wata bukata ta siyasa.

Sai dai APC ta musanta zargin.

A watan jiya aka sace matan, lamarin da ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami'an tsaron Najeriya.

A wancan lokacin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sace 'yan matan a matsayin wani bala'i da ya shafi kasar baki daya.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

2018

 • Ranar 19 ga Fabrairu

  Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hari a makarantar sakandaren mata ta kwana a Dapchi jihar Yobe da ke arewa maso yammacin Najeriya.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 22 ga Fabrairu

  Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe inda ta nemi afuwa kan sanarwar da ta bayar cewa sojoji sun ceto 'yan matan Dapchi.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • 23 ga Fabrairu

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana sa ce 'yan matan sakandaren Dapchi a matsayin wani bala'i da ya shafi kasa baki daya.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 25 ga Fabrairu

  Rundunar Sojin sama ta sanar da tura jiragen yaki da karin dakaru domin bincike da kuma ceto 'yan matan da aka sace.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 26 ga Fabrairu

  An samu sa'insa tsakanin Sojoji da 'Yan sanda kan wadanda alhakin tsaron Dapchi ya rataya a kan wuyansu, inda 'yan sanda suka ce ba da saninsu sojoji suka fice ba.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 27 ga Fabrairu

  Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti na mutum 12 domin binciken yadda aka sace 'yan matan Dapchi 110.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 1 ga Maris

  Majalisar wakilai ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike game da yadda aka sace 'yan matan sakandaren garin Dapchi.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 12 ga Maris

  Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta zabi ta sasanta da Boko Haram maimakon yin amfani da karfin soja domin ceto 'yan matan a raye.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 14 ga Maris

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 19 ga Maris

  Kafar yada labarai ta Amurka ta Wall Street Journal, WSJ, ta ce ta samu bayanan da suka tabbatar mata da cewa bangaren Abu Musab Abu Musab al-Barnawi ne suka sace 'yan matan 110.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 20 ga Maris

  Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da yin biris da gargadin cewa 'yan Boko Haram za su kai hari sa'o'i kalilan gabannin a sace 'yan matan sakandaren Dapchi sama da 100, zargin da sojojin suka musanta.

  Za ku iya karanta karin a nan.

 • Ranar 21 ga Maris

  Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa ta biya kudin fansa domin a saki 'yan Matan makarantar sakandaren garin Dapchi da Boko Haram ta sace.

  Za ku iya karanta karin a nan.

Labarai masu alaka