Amurka ta tuhumi Iran da 'satar bayanan jami'o'i 320'

A man types on a computer keyboard in Warsaw in this February 28, 2013 illustration file picture. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana tuhumar kamfanin Mabna da satar bayanai daga jami'o'i 320

Kasar Amurka ta saka wa wani kamfanin Iran da wasu mutane 10 takunkumi domin tuhumar da take yi musu na yin kutse a na'urorin komfuta da suka hada da daruruwan jami'o'i.

Kamfanin Mabna Institute na fuskantar tuhumar cewa ya saci terabyte 31 na bayanai "masu daraja mallakin jami'o'in".

Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta ce kamfanin ya yi wa jami'o'i 320 kutse a sassa daban-daban na duniya da suka hada da gomman kamfanoni da wasu ma'aikatun gwamnatin Amurka.

Tara daga cikin wadanda ake tuhuma na fuskantar wasu tuhume-tuhumen da ke da alaka da aikata irin wadannan laifukan.

Kuma mutane biyu da suka kafa kamfanin na cikin wadanda ake tuhumar, kuma Amurka na iya kwace kaddarorinsu.

An dai kafa kamfanin Mabna Institute ne a 2013, kuma masu shigar da kara na ganin an yi haka ne domin taimakawa Iran yin bincike da satar bayanai.

Ana tuhumar kamfanin da kai hare-hare ta yanar gizo zuwa jami'o'i 144 a cikin Amurka da 176 a wasu kasashen daban.

Kasashen sun hada da Birtaniya da Jamus da Kanada da Isra'ila da kuma Japan.

Labarai masu alaka