Buhari ya yi wa 'yan Boko Haram tayin afuwa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tayin afuwa ga mayakan Boko Haram idan suka amince za su ajiye makamansu.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Juma'a lokacin da 'yan gana da 'yan matan sakandaren Dapchi da mayakan na Boko Haram suka sako a fadarsa.

Shugaban kasar ya ce tashin hankalin da kasar ke ganin ya ishe ta haka.

Shugaba Buhari ya kuma gargadi hukumomin tsaron kasar da su tabbatar sun samar da cikakken tsaro a duk makarantun da ke fuskantar barazanar harin daga masu tayar da kayar baya.

A wata hira da BBC ministan harkokin cikin gida na Najeriyar Abdurrahman Bello Dambazau ya ce za'a dauki kwararan matakai na ganin an aiwatar da umarnin shugaban kasar.

Abin da ya faru tun sace 'yan Matan

Hakkin mallakar hoto GGSS
 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace 'yan matan
 • Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
 • Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce

Labarai masu alaka