Congo ta yi watsi da taron agaji

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan 13 'yan kasar ne ke matukar bukatar agaji Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan 13 'yan kasar ne ke matukar bukatar agaji

Jamhuriyar Demukradiyyar Kongo ta sanar da cewa ba zata halarci taron neman agaji da aka shirya yi a Geneva a wata mai zuwa ba.

An dai shirya taron ne da nufi tattara gudummuwar kusan dala biliyan biyu da Majalisar Dinkin Duniya ta ce domin a tallafa wajen shawo kan babban bala'i mafi muni na jinkai.

Sai dai Firai ministan kasar Jose Makila ya zargi Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomin agaji da batawa kasar sa suna.

Ya ce duk da cewa kasar sa na cikin wani yanayi, ayyana bukatar neman agajin gaggawa na sanyaya guiwar masu son zuwa kasar don su zuba jari.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce fiye da mutum miliyan 13 'yan kasar ne ke matukar bukatar agaji, inda kusan mutum miliyan hudu da rabi suka fice daga kasar, adadin daya rubunya wadanda suka fice a bara.

Labarai masu alaka