Fursunoni sun kammala digiri a gidan yari

Kimanin fursunoni dubu biyar ne a Uganda suka yi rijistar yin karatun a fannonin dabam dabam

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kimanin fursunoni dubu biyar ne a Uganda suka yi rijistar yin karatun a fannonin dabam dabam

A kasar Uganda wasu fursunoni uku sun samu shaidar digiri kammala karatun lauya daga wata jami'a dake London.

An dai ba fursunonin takardar shaidar kammala karatun su a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a gidan yari dake birnin Kampala.

Daya daga cikin fursunoni uku mace ce, wacce aka yankewa hukuncin daurin rai da rai amma daga bisani ta yi nasarar kalubalantar hukuncin da aka yanke mata.

An dai bayyana cewa matar ta kammala karatun ta na digiri ne ba tare da taje aji an koyar da ita ba, inda a mafi yawan lokuta ta rika yin karatun ta karkashin bishiya a gidan yarin.

Kimanin fursunoni dubu biyar ne a Uganda suka yi rijistar yin karatun a fannonin dabam dabam, kuma ana kallon bangaren kula da gidajen yari na kasar a matsayin mafi ci gaba a nahiyar Afrika.