Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da 'yan Afirka a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Talata an hango wannan yaron dan kasar Congo a cikin sansanin 'yan gudun hijirar Kalemie da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo. Rikicin kabilancin da ake yi a kasar ya tilasta wa sama da mutum 67,000 tserewa daga gidajensu.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu tallata kayan kawa sun baje kolinsu a gaban wakilin hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya a Afirka ta Kudu, mai tsara kayan kawa Gavin Rajah lokacin bikin nunin kayan kawa na duniya da aka yi a Cape Town.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani mutum yana gyara kaya a cikin kwale-kwalen da ke dauke da masu yawon bude ido yayin da rana ta kusa faduwa a tsibirin Lamu da ke Kenya.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A nan kuma wasu daga cikin 'yan matan makarantar Dapchi ne da aka sako suke shiga jirgi a sansanin sojin sama da ke Maiduguri, Nigeria.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsoffin fursunoni ne a nan suka hau kan mota bayan an fitar da su daga gidan yarin Mpimba da ke Bujumbura, babban birnin Burundi bayan Shugaban kasar ya yi musu afuwa.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabannin kasashen Afirka ne nan ke daukar hoto bayan kammala taron da kungiyar tarayyar Afrika ta shurya kan kafa harkar kasuwanci maras shinge a Kigali, Rwanda ranar Laraba. Kasashe goma, ciki har da Najeriya wacce ta fi kowacce kasa karfin tattalin arziki, ba su shiga yarjejeniyar ba saboda tsoron cewa hakan ka iya sa 'yan kasashensu rasa aiki.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magoya bayan Sfax na karkada tutoci lokacin wasan sada zumuntar da suka yi da tsoffin 'yan wasan duniya na Faransa domin bikin cika shekara 90 na kulob din kwallon kafar Tunisia a filin wasan Mhiri da ke Sfax
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ratayawa wannan ragon lambar yabo bayan ya yi nasara a gasar da aka yi a Misrata da ke Libya.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarauniyar kyau ta zabaya ta Zimbabwe Sithembiso Mutukura ta karbi furanni bayan an nada tana kan matsayin a Harare. 'yar shekara 22 ta doke 'yan takara 12 da suka fafata a gasar, wace aka shirya da zumma rage nuna kyamar da ake yi wa zabaya.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan yaron masunci dan kasar Congo yana nade tarunsa a gefen kogin Tanganyika da ke Kalemie a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bayan an sheka ruwan sama a kusa da Manambonitra da ke Madagascar ranar Lahadi.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wannan matar tana zuba ruwa a cikin bokiti a Abidjan, babban birnin Ivory Coast, ranar Laraba kafin bikin ranar Ruwa ta Duniya.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani malamin coci dan kasar Sudan ta Kudu ya gudanar da taron ibada a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Obo na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ranar Juma'a. Daga 2016 zuwa yanzu, fiye da mutum 2,000 suka tsallaka iyaka domin guje wa rikici a Sudan ta Kudu.

Mun samu hotunan ne daga AFP, Reuters, EPA da kuma Getty Images