Hankalinmu a tashe yake — mahaifin 'yar Dapchi

Some of the newly-released Dapchi schoolgirls are pictured in Jumbam village, Yobe State, Nigeria March 21, 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters

Mahaifin 'yar makarantar Dapchi Leah Sharibu, wacce ita kadai ce mai bin addinin Kirista da 'yan Boko Haram suka ki saki, ya ce suna cikin tashin hankalin rashin ganin 'yarsu har yanzu.

Ranar Asabar ne aka tabbatar wa Nathan Sharibu cewa a saki Leah kuma tana kan hanyar zuwa Dapchi domin saduwa da 'yan uwa da danginta.

Sai dai ya shaida wa BBC cewa har yanzu ba a mika musu 'yar tasu ba "kuma labarin da na ji ya tayar min da hankali."

A cewarsa, gwamnati da jami'an tsaro ba su tuntube shi don sanar da shi halin da 'yarsa ke ciki ba.

"Babu wanda ya tuntube ni, ban yi magana da kowa ba; babu wanda ya sanar da ni halin da take ciki", in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar an saki 'yarsa sannan ta ba shi damar ganawa da ita "domin hakan ne kawai zai sa hankalina ya kwanta."

Ranar Laraba ne aka saki 'yan matan 106 da kuma namiji daya, amma aka ki sakin Leah Sharibu saboda ta ki amincewa ta karbi kalmar shahada.

Lamarin ya jawo wa Boko Haram suka sosai daga wurin 'yan kasar, musamman Musulmi wadanda suka ce addinin Musulunci bai amince a tursasawa wani ko wata shiga cikinsa ba.

Da yake ganawa da 'yan matan da aka saka ranar Juma'a, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin bakin kokarinsa wurin ganin an saki Leah Sharibu.

A watan jiya ne mayakan kungiyar suka kai hari garin na Dapchi inda suka je makarantar matan suka kwashe su.

Da farko gwamnatin jihar ta ce dukkan matan sun kubuta amma daga bisani ta janye maganar sannan ta nemi afuwar iyayen yaran.

Shugaba Buhari ya bayyana sace matan a matsayin wani babban bala'i da ya aukawa kasar.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai matan Abuja a cikin jirgin sama
 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace 'yan matan
 • Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
 • Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce
 • Sun gana da Shugaba Buhari

Jam'iyyar PDP mai hamayya a kasar ta yi zargin cewa jam'iyyar APC da fadar shugaban kasa ne suka kitsa sace matan domin cimma burin siyasa.

Sai dai APC ta musanta zargin, tana mai cewa idanun PDP sun rufe ta kasa fahimtar irin nasarar da take samu a yaki da Boko Haram.

Labarai masu alaka