Kun san mutanen da 'suka yi wa Buhari magudin zabe a 2007'?

Scrutineers organise ballots papers on election day, 21 April 2007, in Lagos, Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin ya yi ikirarin yin cuwa-cuwa a zaben Najeriya na 2007

Wasu takardu da BBC ta samu sun nuna cewa kamfanin nan mai tattara bayanai kan zabuka Cambridge Analytica ya taba cika bakin cewa ya yi tasiri kan zabukan kasashen duniya.

Cambridge Analytica ya tsinci kansa a cikin ce-ce-ku-ce saboda ikirarin da aka yi cewa ya yi amfani da bayanan miliyoyin masu amfani da shafin Facebook domin cimma burin siyasa.

Kafar watsa labaran BBC ta ga wasu takardu da kamfanin SCL Elections da ke tattara bayanai da bincike kan zabuka, wanda uba ne ga Cambridge Analytica, ya tattaro gababin shekarar 2014.

Misali, a cikin bayanan, kamfanin ya yi ikirarin shirya zanga-zanga a Najeriya domin rage goyon bayan da 'yan hamayya ke da shi a shekarar 2007.

Marigayi Umaru 'Yar Adu ne ya lashe zaben, yayin da Janar Muhammadu Buhari ya zo na biyu kuma ya kalubalanci sakamakonsa a gaban kotu.

Ofishin harkokin wajen Burtaniya ya ce ba shi da masaniya kan wannan zargi kafin gwamnatin kasar ta bai wa SCL kwantaragi a shekarar 2008.

Cambridge Analytica ya ce yana duba zarge-zargen da aka yi kan SCL.

Takardun sun nuna ikirarin da SCL Elections ya yi cewa duk masu son ya yi hulda da su za su iya tuntubarsu ta hanyar amfani da "kowanne ofishin jakadancin Burtaniya".

Ya kuma yi ikirarin cewa ma'aikatar tsaron Burtaniya ta amince da ayyukansa.

Takardun sun bayyana yadda SCL Elections ya shirya zanga-zangar "kin gudanar da zabe" domin rage goyon bayan da jam'iyyun hamayya ke da shi a 2007. Kungiyar tarayyar Turai da ta sanya ido kan zaben ta bayyana shi a matsayin daya daga cikin marasa inganci da aka gudanar a kasar.

Kazalika takardun sun nuna yadda SCL Elections ya yi amfani da bambancin kaliba da Latvia ke fama da shi wajen taimaka wa masu hulda da shi a zaben 2006.

SCL ya yi ikirarin cewa gabanin zaben 2010 a kasar Trinidad and Tobago ya kaddamar da "gagarumar farfagandar siyasa kan matasa" ta yadda suka amince cewa jam'iyyar da yake wa aiki tana son hada kansu.

Labarai masu alaka