Paul Biya: Shugaban da ke 'mulkin kasarsa daga kasashen waje'

President of Cameroon Paul Biya meets with Chinese President Xi Jinping (not pictured) at The Great Hall Of The People on March 22, 2018 in Beijing, China. Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya shafe fiye da shekara 35 a kan mulki. Kuma a yayin da 'yan kasar ke tattaunawa kan shekarun da ya kwashe yana mulki, a kasashen waje kuwa an fi mayar da hankali ne kan yadda ba ya zama a kasar- kamar yadda Paul Melly, wani manazarci a Chatham House, ya yi bayani.

Paul Biya yana shan suka kan yadda ake ganin yana wakilta wasu suna mulkin kasarsa maimakon ya gudanar da aikin da ke rataye a wuyansa.

Kwanakin baya dai ya jagoranci taron ministoci, karon farko cikin sama da shekara biyu.

A watan Oktoba za a gudanar da zaben shugaban kasa kuma 'yan kasar ta Kamaru sun kasa kunne su ji ko Mr Biya, dan shekara 85, zai sake tsayawa takara. Sai dai ba a yi bayani kan hakan ba lokacin taron ministocin.

Tun shekarar 1982 ya hau kan mulki, abin da ya sa ya zama daya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa a kan mulki. A lokacin mulkinsa, Kamaru ta fice daga kangin tabarbarewar tattalin arziki sannan ta sauya daga kasa mai jam'iyya daya zuwa mai jam'iyyu da dama.

Sai dai gwamnatinsa cike take da cin hanci da kuma kawo koma-baya, lamarin da ya sa a 2008 ta yi watsi da wa'adin mulkin da aka sanya a kudin tsarin mulki, abin da ya ba Mr Biya damar sake tsayawa takara a zaben 2011.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Biya ya je China a makon jiya

Al'amura na sauyawa a Afirka. Ana samun raguwar shugabannin da kan kwashe shekara da shekaru a kan mulki. Talabijin da ke amfani da tauraron dan adam da kuma samuwar intanet sun nuna yadda ake samun sauyin mulkin dimokradiyya a kasashen Afirka, kudu da hamadar sahara.

Kashi 60 na 'yan kasar Kamaru 'yan kasa da shekara 25 ne don haka ba a haife su ba lokacin da Shugaba Biya ya soma mulki. Ana matukar bukatar ayyukan yi da bunkasar rayuwa a Kamaru.

Jam'iyyar hamayya ta Social Democratic Front ta fahimci halin da ake ciki. A farkon shekarar nan shugabanta, John Fru Ndi, mai shekara 76, ya sauka daga mukaminsa domin bayar da dama ga matasa, inda aka zabi wani dan kasuwa mai shekara 49 kuma tsohon matukin jirgin sama, Joshua Osih, domin ya tsaya wa jam'iyyar takara.

Otal din Switzerland

Wannan shi ne babban kalubalen da ke fuskantar Mr Biya a yayin da zai yanke hukunci kan ko zai sake tsayawa takara ko kuwa zai fasa.

Rashin zamansa a cikin kasar yana batawa 'yan hamayya rai.

Tafiye-tafiyen da yake yawan yi su ne manyan batutuwan da aka jaridar gwamnati Cameroon Tribune da kungiyar masu yaki da cin hanci da rashawa ta The Organised Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP suka fi tattaunawa a kai a shafukan intanet. Kungiyar na bayar da bayani a kullum kan adadin kwanakin da shugaban ya kwashe ba ya kasar.

The OCCRP ta kiyasta cewa shugaban kasar ya kwashe kusan kwana 60 yana ziyarar kasashen waje ta kashin kansa a shekarar da ta wuce.

Kungiyar ta yi zargin cewa ya kwashe kashi uku cikin hudu na shekarar 2006 da 2009 a kasshen waje. An yi amannar cewa Mr Biya ya fi zama a otal din The Intercontinental da ke Geneva.

Sai dai jaridar gwamnati ta Cameroon Tribune ta ce binciken da kungiyar The OCCRP ta yi "na cike da farfagandar neman cin zabe".

Hakkin mallakar hoto AFP

Acan kasarsa kuwa, Shugaba Biya ya zabi gudanar da mulki ta yi amfani da salon rashin fitowa bainar jama'a, inda wasu lokutan yakan tafi kauyensu.

Ya mika dawainiyar gudanar da mulki ta yau da kullum a hannun Fira Minista, Philemon Yang, wanda a kowanne wata yake gudanar da taron "majalisar ministoci".

An bai wa Firai Ministan damar sanya ido kan ministoci, yayin da shugaban kasa ke ganawa da manyan jami'an gwamnati a kadaice cikin fadarsa da ke Yaoundé.


Gawasu karin labaran da za ku iya karantawa:


Mika jagorancin kasar da Mr Biya a hannun wasu mutane ya sa yana shan suka saosai a wurin 'yan hamayya wadanda ke kiransa da suna "shugaban da ba ya zama a kasarsa".

Wannan rashin zama ya kara fito da bambancin da ke tsakanin bangaren Kamaru da ke magana da turancin Ingilishi da kuma bangaren da ke amfani da Faransanci. Shugaba Biya, kamar mutumin da ya gada Ahmadou Ahidjo, ya fito ne daga yankin da ke amfani da Faransanci, yayin da ake nada Firimiya daga yankin da ke amfani da Ingilishi.

Wani mai sharhi a kasar ya ce ana kallon shugaban a matsayin wanda ke barin shugaban gwamnati yana gudanar da aiki.

Don haka ana ganin duk lokacin da ya kira taron majalisar zartarwa a matsayin wani taro na musamman.

Taron da ya gudanar kwanakin baya na musamman ne saboda an yi shi ne bayan yin garambawul ga majalisar ministoci. Ya yi kama da wanda aka gudanar a 2015, wanda aka yi jim kadan bayan gudanar da sauye-sauye kan majalisar gwamnatin kasar.

A wannan karon an yi tsammani Mr Biya zai sanar da aniyarta ta sake tsayawa takara a zaben da ke tafe ko kuma ya fasa tsayawar amma bai nuna wata alama ba.

Sai dai duk da haka taron abin tattaunawa a kansa ne.

Bambancin harshe

Yankunan Arewa maso yama da Kudu maso yammacin Kamaru da ke amfani da Ingilishi sun kwashe fiye da shekara daya suna tarzoma.

Lauyoyi da malaman makarantu ne suka soma zanga-zanga inda suka bukaci a inganta rayuwar mutanen da ke zaune a yankunan.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Zanga-zanga a yankuna da ke amfani da Ingilishi

Sai dai lamarin ya kazance har ta kai ga taho-mu-gama tsakanin jami'an tsaro da kuma toshe intanet na kwana 93 a yankuna da ke magana da turancin Ingilishi da kuma kafa kungiyar a-ware ta "Ambazonia", inda aka yi kashe-kashe.

Gwamnati ta dauki matakin kawo karshen wannan matsala, sai dai cike take da hatsari. Burtaniya da Faransa sun yi kiran a sasanta.

Shugaba Biya ya mayar da martani ta hanyar yin garanbawul ga majalisar zartarwarsa ranar biyu ga watan Maris, abin da ke nuna cewa ya dauki matakin a-ciza-a-hura.

Labarai masu alaka