Ana gudanar da zaben 'yan majalisar dattawa a Kamaru

Zaben Kamaru

Ranar Lahadi ne ake gudanar da zaben 'yan majalisar dattawa a Kamaru.

'Yan takara daga jam'iyun siyasa tara ne, cikinsu da RDPC da take kan mulki, ke zawarcin kujera 70 na zababbun sanatocin wadanda kansaloli, 9,600 ne ke jefa musu kuri'u.

Wannan a karo na biyu kenan ake gudanar da zaben tun kafa mulkin dimokradiyya a Kamaru.

Daga bisani ne kuma Shugaban kasa zai nada wasu 30 da za su cika adadin sanatoci 100 da majalisar za ta kunsa.

Babbar jam'iyar adawa ta SDF - wadda itace ta biyu a majalisar da wa'adinta yake karewa nan gaba wasu 'yan kwanaki - tana zawarcin kuri'un kansaloli a larduna biyar kawai.

Bayan kotun tsarin mulki ta soke jerin sunayen 'yan takaranta a larduna biyu ita uwar jam'iyar ta janye 'yan takaranta a lardi guda.

Hakan ya sa jam'iyar UNDP ce ta biyu wurin neman lashe kuri'un kansaloli bayan jam'iyar RDPC mai mulki wadda ta tsaida 'yan takara a duk larduna 10 na kasa.

Su ma kansalolin da ke jefa kuri'a, jama'a sun zabesu ne karkashin jam'iyun siyasa.

Labarai masu alaka