An mika 'yan matan Dapchi hannun iyayensu

'Yan matan suna cikin nutsuwa
Image caption 'Yan matan suna cikin nutsuwa, in ji iyayensu.

Gwamnatin Najeriya ta mika 'yan matan makarantar Dapchi 106 da kuma namiji daya a hannun iyayensu ranar Lahadi.

Iyayen wasu daga cikin 'yan matan sun shaida wa BBC cewa sun tarbi 'ya'yan nasu cikin murna da annashuwa.

A cewar Malam Adamu Gashuwaram, 'yarsa ta isa gida cikin nutsuwa sabanin lokacin da mayakan Boko Haram suka mayar da su garin.

Mahaifiyar daya daga cikin 'yan matan ta gaya wa BBC cewa an tabbatar mata da zuwan 'yarta cikin garin amma tana jiran isarta gida.

"Gida ya cika da murna inda kowa ke dakon shigowarta," in ji ta.

Sai dai mahaifin Leah Sharibu, wacce ita kadai ce mai bin addinin Kirista da 'yan Boko Haram suka ki saki, ya ce suna cikin tashin hankalin rashin ganin 'yarsu har yanzu.

Ranar Asabar ne aka tabbatar wa Nathan Sharibu cewa a saki Leah kuma tana kan hanyar zuwa Dapchi domin saduwa da 'yan uwa da danginta.

Ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar an saki 'yarsa sannan ta ba shi damar ganawa da ita "domin hakan ne kawai zai sa hankalina ya kwanta."

Ranar Laraba ne aka saki 'yan matan 106 da kuma namiji daya, amma aka ki sakin Leah Sharibu saboda ta ki amincewa ta karbi kalmar shahada.

Lamarin ya jawo wa Boko Haram suka sosai daga wurin 'yan kasar, musamman Musulmi wadanda suka ce addinin Musulunci bai amince a tursasawa wani ko wata shiga cikinsa ba.

Da yake ganawa da 'yan matan da aka saka ranar Juma'a, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin bakin kokarinsa wurin ganin an saki Leah Sharibu.

A watan jiya ne mayakan kungiyar suka kai hari garin na Dapchi inda suka je makarantar matan suka kwashe su.

Da farko gwamnatin jihar ta ce dukkan matan sun kubuta amma daga bisani ta janye maganar sannan ta nemi afuwar iyayen yaran.

Shugaba Buhari ya bayyana sace matan a matsayin wani babban bala'i da ya aukawa kasar.

Hakkin mallakar hoto Amsami Ali
Image caption An kai matan Abuja a cikin motoci
 • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
 • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
 • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
 • An shiga rudani kan sace 'yan matan
 • Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
 • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
 • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
 • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
 • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
 • Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
 • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce
 • Sun gana da Shugaba Buhari

Jam'iyyar PDP mai hamayya a kasar ta yi zargin cewa jam'iyyar APC da fadar shugaban kasa ne suka kitsa sace matan domin cimma burin siyasa.

Sai dai APC ta musanta zargin, tana mai cewa idanun PDP sun rufe ta kasa fahimtar irin nasarar da take samu a yaki da Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto Amsami Ali
Image caption Sun kwashe sama da wata daya a hannun mayakan Boko Haram

Labarai masu alaka