Sojojin Nigeria sun yi wa TY Danjuma raddi

Rundunar sojin ta ce ita ce ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasar. Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY TWITTER
Image caption Rundunar sojin ta ce ita ce ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasar.

Rundunar sojin Najeriya ta yi Alla-wadai da kalaman tsohon hafsan sojin kasar Laftanar Janar Theophilus Yakubu Danjuma inda ya ce sojojin kasar ne ke mara wa 'yan bindiga baya wajen kawar da al'ummu a jihar Taraba.

Shi dai Janar Theophilus Danjuma mai ritaya ya yi kalaman ne yayin bikin yaye daliban jami'ar jihar Taraba da ke Jalingo ranar Asabar.

Ya shawarci al'ummar Najeriya da su tashi tsaye su kare kansu daga hara-haren makiyaya.

Janar Danjuma ya ce "zaman lafiya a jihar Taraba na cikin wani hali kuma akwai kokarin shafe wata al'umma a jihar, a don haka wajibi mu tashi tsaye."

Tsohon hafsan sojin ya ce idan jama'a suka zura ido suna jiran sojoji su kare su to za a kashe su daya bayan daya.

Tuni dai rundunar sojin Najeriyar a wata sanarwa, ta mayar da martani ta bakin mai magana da yawunta, Birgediya Janar Texas Chikwu.

Rundunar ta yi Alla-wadai da kalaman tsohon hafsan inda ta jaddada cewa rundunar sojin kasar ce ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasar.

Rikicin manoma da makiyaya

Rikicin manoma da makiyaya dai a Najeriya ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu, al'amarin da ya jawo hankalin kusan daukacin 'yan Najeriya.

Rikicin ya fi kamari ne a jihohin Filato da Benue da Taraba da Nassarawa da Kaduna.

A baya gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.

Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan kira, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar domin kiwo.

Amma a watan Fabrairu Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gayyaci Fulani makiyaya su koma jiharsa domin gudanar da kiyo ba tare da samun matsala ba.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka