Abin da ya sa za mu yi sulhu da Boko Haram - Lai Mohammed

Lai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ministan ya ce mutane da dama ba su san cewa sun dade suna tattaunawa da mayakan kungiyar kan tsagaita wuta ba

Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce gwamnatin kasar ta fara tattauna wa da kungiyar Boko Haram a kan yiwuwar tsagaita wuta, da fatan kawo karshen rikicin na dindindin.

A ranar Lahadi ne Mista Mohammed ya fadi hakan yayin wata ganawa ta musamman da ya yi da manema labarai a Legas, domin yi musu karin haske kan yadda aka ceto 'yan matan Dapchi.

A wata sanarwa da ya aike don karin haske kan batun sakon yaran, Ministan ya ce: "Mutane da dama ba su san cewa mun dade muna tattaunawa da mayakan kungiyar kan tsagaita wuta ba."

Mista Mohammed ya ce tun ranar 19 ga watan Maris ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda, domin a samu damar dawo da 'yan matan.

Wannan ne karo na farko cikin shekaru 10 da suka gabata da gwamnati ta ce tana tattaunawa da Boko Haram kan tsagaita wuta, a rikicin tayar da kayar bayan da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tun shekarar 2009.

Gwamnatin kasar karkashin shugabancin Muhammadu Buhari dai ta sha nanata cewa a shirye take ta hau teburin sulhu da kungiyar.

Wannan ci gaba dai na zuwa ne jim kadan bayan dawowar 'yan matan sakandaren Dapchi fiye da 100 da mayakan Boko Haram suka sace.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A karshen makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya gana da 'yan matan Dapchi bayan dawo da su da mayakan BH suka yi

A ranar Lahadi ne aka mayar da 'yan matan wajen iyayensu bayan sun gana da Shugaba Buhari a Abuja, bayan sun shafe wata guda a hannun Boko Haram.

Sai dai har yanzu akwai sauran yarinya daya a hannun mayakan kungiyar, wacce suka ce ba su dawo da ita ba ne saboda kin musulunta da ta yi, yayin da wasu 'yan matan biyar kuwa suka hadu da ajalinsu a can.


Sharhi

A iya cewa wannan wani muhimmin ci gaba ne daga gwamnatin Najeriya. A baya Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa ba zai hau teburin sulhu da mayakan ba.

Amma a wani al'mari mai kama da sauya ra'ayi na farat daya, sai ga Ministan watsa labaran kasar ya ce gwamnati ta jima tana tattaunawa da su.

Sai dai kuma ministan bai yi karin haske kan da wanne bangare na kungiyar ake tattaunawa ba, bai kuma yi bayanain irin yarjejeniyar da ake kullawa ba.

Wani mai sharhi a Najeriya Antony Goldman, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, zai yi wahala a yi sulhu da kungiyar saboda rabuwar da ta yi bangare biyu.

Boko Haram dai ta balle ne a lokacin da kungiyar IS ta bayyana Abu Musab al-Barnawi, a matsayin shugaban kungiyar a watan Agustan 2016.

Daya bangaren kuma karkashin jagorancin Abubakar Shekau shi aka fi sani a matsayin shugaban kungiyar.

An san shi wajen fitowa a bidiyo da yake kalubalantar hukumomin Najeriya, kuma bangarensa ne yake amfani da 'yan mata don kai hare-haremn kunar bakin wake.

Goldman ya shaida wa Reuters cewa: "Akwai bangarori da dama wadanda ke aikata mugayen ayyuka kuma suna yi wa duniya kallo da wani tsari da ya sabawa tsarin dokoki da kuma dimokradiyya - amma kuma akwai wasu bangarori da ke shirye don yin sulhu da su."


Boko Haram a takaice

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau shi ne shugaban Boko Haram tun 2009
 • An kafa ta a shekarar 2002
 • Sunanta da Larabci shi ne, Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad
 • Ta fara aikinta ne da nuna kin jinin karatun boko
 • Ta kaddamar da kai hare-hare a shekarar 2009 da zummar samar da daular musulunci
 • Amurka ta ayyana ta a matsayin kungiyar ta'adda a 2013
 • Kungiyar ta ayyana wasu yankuna da ta kame a matsayin daulolin musulunci a shekarar 2014
 • A yanzu haka sojoji sun kwato mafi yawan yankunan
 • Suna ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake
 • Tana ayyukanta a Najeriya da Kamaru da Nijar da Chadi
 • Ta rabu biyu tsakanin bangaren Shekau da na Al-barnawi
 • Dukkan bangarorin biyu sun taba sace 'yan matan makarantar sakandare na Chibok da Dapchi

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka