'Yan sandan Najeriya makaryata ne - Dino Melaye

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar Dino kan takun sakarsa da 'yan sanda

Ku latsa alamar hoton da ke sama don jin martanin da Dino ya mayar kan artabunsa da 'yan sanda:

Ana ci gaba da kiki-kaka tsakanin dan majalisar dattawan Najeriya Dino Melaye da rundunar 'yan sandan kasar, wadda ta yi ikirarin cewa za ta ayyana shi a cikin jerin mutanen da take nema ruwa-a-jallo.

Rundunar ta yi ikirarin daukar wannan mataki ne, sakamakon zargin cewa an nemi ya gurfana gaban wata kotu a Lokoja bisa tuhumar da ake masa ta taimakawa wajen aikata miyagun ayyuka da suka shafi fashi da makami da satar mutane a jihar Kogi, ta hanyar bai wa wasu matasa bindigogi.

A halin da ake ciki dai, kotu ta tsayar da ranar Laraba mai zuwa don sauraron shari'ar.

Sai dai Sanata Melaye ya ce rundunar 'yan sandan karya take yi don ba a taba gayyatarsa zuwa kotu ba, sai a kafafen watsa labarai ya ji labari.

"Batun da aka ce wai sufeto janar na 'yan sanda ya ce na je kotu ranar 20 ga wata, to ai ni a wannan rana ma ba na nan, ina Ghana tare da wasu sanatoci 'yan uwana kan wani taro na harkar mai.

"Don haka ni ba wanda ya taba ba ni wata gayyata daga kotu, ko a wannan karon ma da suka ce ana nemana ranar 28 ga wata har yanzu ba wanda ya kawo takarda daga kotu cewa ana nemana."

Sanata Melaye ya kuma ce a yanzu haka rayuwarsa na cikin barazana ta yadda ba zai iya zuwa garin Lokojo ba, inda can ne babban birnin jiharsa ta asali, saboda "sau biyu aka nemi a kashe ni a can," in ji shi.

Sai dai tun da fari rundunar 'yan sanda ta yi watsi da wannan zargi na Sanata Melaye inda ta ce bayanan da ya bayar ba su da tushe.

Ku latsa alamar hoton da ke sama don sauraron hirar Sanata Dino Melaye ta kasance tsakaninsa da Ibrahim Isa kan abin da ya hana shi gurfana gaban kuliya da kuma wasan-buyan da yake yi da 'yan sanda a matsayinsa na mai yin doka, inda ya musanta.

Hakkin mallakar hoto Dino Facebook

Dino Melaye a takaice

  • Dan asalin jihar Kogi, amma an haife shi a Kano
  • Shekararsa 44
  • Ya yi karatun firamare a Kano
  • Ya yi digirinsa a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria
  • Yana wakiltar Kogi Ta Yamma a majalisar dattawa
  • Ya taba zama dan majalisar waklilan Najeriya har sau biyu
  • An san shi a tarar aradu da ka a harkokin siyasa
  • Ya taba karbar lamar yabo na dan majalisar wakilan da babu kamarsa daga wata kungiyar matasa

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka