Gobara ta kashe mutum 14 a sansanin 'yan gudun hijra a Borno

Mutum fiye da 200 ne suka mutu a harin bam din da jiragen sojoji suka kai bisa kuskure a jihar Borno da ke Najeriya Hakkin mallakar hoto EPA

Rahotanni sun ce wuta ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Rann, a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wutar ta tashi ne da misalin karfe 10:30 na safe, a ranar Litinin, inda ta shafe sa'o'i kusan uku tana ci.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Injiniya Satomi Ahmad, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce a kalla mutum goma sha hudu sun rasa rayukansu sakamakon gobarar.

Ya kara da cewa wasu da dama kuma sun samu raunuka ciki har da yara.

Jami'in ya ce, gidaje da dama da ke garin da kuma tantunan da 'yan gudun hijrar ke zaune sun kone.

Injiniya Satomi Ahmad, ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon wutar da aka rura don dafa abinci a sansanin.

Tuni dai aka kai wadanda suka samu raunukan asibiti domin karbar magani, kuma hankulan mazauna sansanin ya dan kwanta, kasancewar an kashe wutar.

Shugaban hukumar ta SEMA, ya ce an tura wata tawaga da ta hadar da jami'an hukumar da jami'an kiwon lafiya da kuma jami'an mambobin wani kwamiti da gwamnan jihar ta Borno ya kafa wanda ke duba ayyuykan bayar da agaji a jihar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar sojin Najeriya ta nemi afuwa kan harin da aka kai Rann bisa kuskure a bara

Kusan mutum 40,000 ne ke zaune a garin na Rann, kuma mafi yawancinsu, sun samu mafaka ne bayan da suka bar gidajensu saboda yanayin zaman dar-dar din da ake ciki a yankunansu, sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.

Ba wannan ne karo na farko da wani iftila'i ke afkawa sansanin 'yan gudun hijira na Rann ba, ko a farkon watan nan ma, wasu ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya uku sun rasa rayukansu a yayin da masu tayar da kayar baya suka kai hari wani sansanin sojoji da ke garin.

Wannan lamarin dai ya sa majalisar ta dakatar da ayyukanta a sansanin, wanda kusan mutanen da ke zaune a garin, sun raja'a ne a kan ayyukan wannan kungiyar wajen kula da lafiyarsu.

Kazalika a watan Janairun 2017 ma, mutum 115 ne suka mutu a harin da jirgin yakin Najeriya ya kai bisa kuskure kan sansanin 'yan gudun hijira na Rann din.

Garin Rann a takaice

  • Rann karamin gari ne a jihar Borno
  • Akwai dubban 'yan gudun hijira a garin
  • Hukumomin agaji da dama suna ayyukan jin kai a garin
  • Iftila'i ya sha afkawa garin

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka