An gano wata giwa da ke tauna wuta a Indiya

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon yadda giwa ke tauna wuta tana fidda hayaki

Wani bidiyo da aka dauka a Indiya wanda ya nuna yadda wata giwa take fitar da hayaki daga wutar da ta tauna ya bai wa kwararru a harkar namun daji a kasashen duniya mamaki.

Masanin kimiyya Vinay Kumar, wanda wani dan kungiyar da ke kare namun daji ne a Indiya shi ne ya dauki hoton bidiyon mai tsawon dakika 48 lokacin da suka ziyarci dajin Nagaihole da ke jihar Karnaka a watan Afrilun shekarar 2016.

Ya shaidawa BBC cewa sai yanzu ya fitar da bidiyon saboda bai san "abu ne mai muhimanci ba."

Masana kimiyya sun ce har yanzu ba su san dalilin da ya sa giwar take fitar da hayakin toka ba.

"Wannan shi ne bidiyo na farko kan wata giwa da ke daji, da ta nuna dabi'a irin wannan, kuma wannan ya bai wa masana kimiyya mamaki," a cewar wata sanarwa da kungiyar kula da namun daji a Indiya ta fitar.

Tauna gawayin da ke ruruwa

Mr Kumar ya ce shi da tawagarsa sun kai ziyara daji ne da safe domin su duba kamarorin da suka saka domin daukar hoton damisa.

Ya kuma hango giwar ce daga wani wuri mai nisan mita 50 kuma ya fara daukar hoto da kamararsa.

Giwar na tauna gawayin da ke ruruwa wanda ya ke cikin wutar da aka bari inda take fitar da hayaki daga bakinta," a cewar sanarwar.

"Abin da muka gani a wannan rana ya yi kama da giwar da take shan taba - za ta sa gawayi kusa da bakinta, inda take fitar da bakin hayaki,"a cewar Mr Kumar.

Masanin giwaye Varun R Goswami, wanda ya yi nazari kan bidiyon, ya yi amannar cewa "watakila giwar na son ta tauna gawayin ne, yayin da ta ke kokarin daukar wani abu daga kasa, inda take fitar da hayakin da ke tare da abin da ta dauka, tana hadiyyar sauran.

"Bakin gawayi na da sinadarin Toxin, sai dai duk da cewa ba shi da abubuwa masu gina jiki, amma yana jan hankalin namun daji saboda yana yi musu magani," a cewarsa.

Labarai masu alaka