Kwatanta albashinku da na sanata a Najeriya a wannan kalkuletar

'Yan Najeriya da dama sun kadu bayan da suka ji yawan kudin da 'yan majalisar dattawa ke samu.

Sanata Shehu Sani ne ya bankada hakan inda ya ce sanatoci na karbar naira miliyan 13.5 duk wata, ya rubanya albashinsu na wata kusan sau 20.

Idan aka hada albashin da kudin da suke samu, ta yaya za ku kwatanta albashinku da na sanatan Najeriya.

Duba hakan ta hanyar amfani da kalkuletarmu.

Sanata a Najeriya na samun kusa naira miliyan 156 duk shekara.

Idan kana daukar mafi karancin albashi na (N18,000)

 • To cikin sa'a daya da minti daya sanata ke samun abun da ka ke dauka a wata.
 • Da irin albashin da ka ke dauka a yanzu, zai dauke ka shekara 722 da wata uku a kiyasce kafin ka samu abun da sanata ke samu a shekara.
 • Idan ka fara aiki tun shekarar 1296 to da sai a bana ne za ka kamo sanata.
 • Albashin sanata na wata daya, zai sayan buhun shinkafa 866, yayin da albashinka na wata zai iya sayen buhun shinkafa daya kacal.

Idan kana samun N50,000

 • Zai dauki sanata sa'a biyu da minti 49 ya samu abun da ka ke samu a wata.
 • A albashin da ka ke dauka yanzu, zai dauke ka shekara 260 a kiyasce kafin ka samu abun albashin sanata na shekara.
 • Idan ka fara aiki a shekarar 1758, to sai a yanzu ne za ka kamo su wajen samun abun da suke karba.
 • Albashin sanata na wata zai iya sayen buhun shinkafa 866, yayin da albashinka na wata zai iya sayen buhun shinkafa uku kacal.

Idan kana karbar N100,000:

 • Zai dauki sanata sa'a biyar da minti 37 ya samu albashinka na wata.
 • A albashin da ka ke karba yanzu, zai dauke ka shekara 130 a kiyasce kafin ka sanu abun da sanata yake samu a shekara.
 • Idan ka fara aiki a shekarar 1888, to sai a bana ne za ka kamo sanata a yawan abun da ka ke karba.
 • Albashin sanata na wata zai sayi buhun shinkafa 866 yayin da albashinka zai sayi buhun shinkafa shida

Idan albashinka ya kai N150,000:

 • Zai dauki sanata sa'a takwas da minti 26 ya samu albashinka da ka ke samu a wata.
 • A albashin da ka ke dauka yanzu, zai dauke ka tsawon shekara 86 da wata takwas kafin ka samu albashin sanata na shekara daya.
 • Idan ka fara aiki a shekarar 1931 to da sai a yanzu ne za ka kamo sanata a yawan abun da uake dauka.
 • Albashin sanata na wata zai sayi buhun shinkafa 866 yayin da albashinka zai sayi buhun shinkafa 10

Idan albashinka ya kai N200,000:

 • To sanata zai samu irin wannan kudin cikin sa'a 11 da minti 14.
 • A albashin da ka ke dauka yanzu, zai dauke ka tsawon shekara 65 da wata takwas kafin ka samu albashin sanata na shekara daya.
 • Idan ka fara aiki a shekarar 1953 to da sai a yanzu ne za ka kamo sanata a yawan abun da yake dauka.
 • Albashin sanata na wata zai sayi buhun shinkafa 866 yayin da albashinka zai sayi buhun shinkafa 13

Yaya za ka hada kanka da sanata?

Sanya yawan albashinku a nan
Duk bayanan da za ku sa iyakarsu kwamfutarku, BBC ba za ta kai su wani waje ba.

kai/ke kwana 30

Rarraba sakamakonka

Rarraba sakamakonka

Rarraba sakamakonka

Tun lokacin da ka ke kan wannan shafin

Ka samu:

Wadanda suka yi aikin

Shiryawa: Olawale Maloma - Tsarawa: Manuella Bonomi

Yadda aka tsara

Abun da ake hasashen sanatoci na samu ya danganta da kalaman da Sanata Shehu Sani ya yi ne, wanda dan majalisa ne a majalisar dattawa a ranar 7 ga watan Maris, 2018. A yanzu dai an bayyanawa mutane yawan kudin da 'yan majalisar ke karba.

An kiyasta musayar kudin a kan duk dalar Amurka daya kan naira 359 a ranar 20 ga watan Maris ta hanyar amfani da http://xe.com

Kwalkuletar ta dauka cewar ana sayar da buhun shinkafa a kan N15,000

Aika da wannan shafi

Aika da wannan shafi

Labarai masu alaka