Buhari ya hana shugabannin APC yin tazarce

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Facebook/Buhari Sallau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci Babban Kwamitin Zartarwar (NEC) jam'iyya mai mulki ta APC da kada ya sabunta wa'adin shugabannin jam'iyyar.

Lokacin babban taron jam'iyyar a watan jiya ne aka amince da aka kara wa shugabanni wa'adin shekara guda.

Sai dai wadansu daga cikin jagororin jam'iyyar ciki har Mista Bola Ahmad Tunubu sun nuna adawarsu ga hakan.

A jawabin da ya gabatar yayin babban taron jam'iyyar wanda aka yi jiya Litinin, Shugaba Buhari ya umarci dakatar da tsawaita wa'adin shugabannin saboda kaucewa ce-ce-ku-ce kuma yin hakan ya saba wa kudin tsarin jam'iyyar, a cewarsa.

Sai dai yayin da yake ganawa da manema labarai bayan taron,mai magana da yawun jam'iyyar Malam Bolaji Abdullahi ya ce an kafa wani sabon kwamiti wanda zai duba wannan batun.

Har ila yau ya ce ana saran kwamitin zai mika shawarwarinsa akalla zuwa gobe Laraba.

Jam'iyyar APC dai na fama da rikicin cikin gida, musamman a rassan jam'iyyar da ke jihohin kasar.

Kuma wadansu na ganin matakin da shugaban ya dauka ba zai rasa nasaba da karatowar zabukan shekarar 2019 ba.

Karanta wadansu karin labarai

Buhari ya sa Tinubu ya sasanta rikicin APC

Rikici ya barke a jam'iyyar APC

Labarai masu alaka