Ana murnar mutuwar mai kamfanin MMM

Sergei Mavrodi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marigayi Sergei Mavrodi

Akan ce ba a murnar mutuwa, amma wannan karon 'yan Najeriya da dama wadanda suka yi asarar miliyoyin kudadensu, suna ta bayyana murna dangane da mutuwar mutumin nan dan kasar Rasha, Sergey Panteleevich Mavrodi, wanda ya bullo da shirin nan na zamba da a takaice ake kira ''MMM''.

A karkashin shirin jama'a su kan saka jari da nufin a biya su ribar makudan kudi daga jarin da wasu mutanen suka sa daga bisani.

Mista Mavrodi, dan asalin kasar Rasha, ya mutu ne yana da shekara 62 a duniya.

An garzaya da marigayin zuwa wani asibiti ne daga wani wajen shiga mota a daren ranar Litinin, bayan da ya yi korafin wani ciwo a kirjinsa.

Daga nan ya ce ga-garinku-nan da sanyin safiyar Talata.

Mutuwar wannan dan taliki ke da wuya, sai nan da nan labarin ya bazu kamar wutar daji a kafar sada zumunta da musayar ra'ayi ta intanet, inda jama'a daga sassa daban-daban na duniya suke ta tofa albarkacin bakinsu.

Sakamakon yadda mutuwar ta tunatar da dubban jama'a musamman ma kan yadda suka yi asarar miliyoyin kudin da suka saka jari a shirin na neman riba a bagas.

A Najeriya, wani kwararre a fannin harkar yada labarai da ke zaune a birnin Ikko, mai suna Joshua, ya shaida wa BBC cewa kudinsa sun salwanta ke nan a sakamakon mutuwar mutumin da ya bullo da shirin na saka jarin da a takaice aka fi sani da lakabin ''MMM''.

Mista Joshua ya ce ya saka jarin naira 100,000 shekara uku da suka gabata a waccan harka, bayan da wani dan uwansa ya kwadaitar da shi game da batunta.

Ya kuma yi wa marigayin fatan Allah-ji-kan-rai, duk da yake dai abin da ya yi a lokacin da yake raye ba mai kyau ba ne.

Shi kuwa wani, wanda ba ya so a ambata sunansa, cewa ya yi:

Wani abokina ne ya gabatar mani da wannan harka ta ''MMM'', kuma ya tabbatar mani cewa ana samun riba sosai a cikinta, sai na ji ina sha'awar shiga ni ma.

Sai na fara da sanya kudi naira 200,000, kuma da farko komai zakkyau.

Daga nan sai na kara zuba karin jari, ina kara zuba kudi sai aka fara samun matsala.

Na yi asarar dukkan kudina, kuma na rasa kudi kusan naira miliyan hudu.

An rika lasa wa jama'a zuma a baka, cewa za a ba su ribar kashi ashirin da biyar ko ma saba'in da biyar cikin dari na adadin jarin da suka saka.

Inda mutanen da suka saka jari da farko suka rika karbar kudadensu da ribarsu yayin da wasu sababbin masu saka saka jari suka biya kudi a kasashen Australia da Brazil da Ghana da Indiya da Kenya da Afirka ta Kudu da kuma Najeriya.

Mutane kimanin miliyan 2.5 ne suka shiga wannan harka mai kama da wala-wala, yayin da aka kaddamar da shafinta na intanet a Najeriya a cikin shekarar 2015.

Ko da yake kungiyoyi da hukumomin gwamnati da shugabannin addini sun ja kunnen wa jama'a hadarin da ke tattare da shiga waccan harkar, kafin daga karshe lamarin ya koma irin abin nan da akan ce ''Garin neman kiba an samo rama'', bayan da sababbin masu saka jari suka shiga nokewa.

Kimanin mutum miliyan goma ne suka yi asarar kudadensu, a karshe kuma kasashe da dama sun dakatar da gudanar da harkar ta ''MMM''.

Mavrodi dai, wani tsohon dan majalisar dokoki ne na kasar Rasha, wanda aka zartar wa daurin shekara hudu da rabi a gidan maza, bayan da ya damfari miliyoyin Rashawa.

Labarai masu alaka