'Koriya ta Arewa za ta dakata da shirin nukiliya'

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da takwaransa na China Xi Jingping Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana ganin ganawar shugabannin biyu sharar fage ce ta haduwar Kim Jong-un da takwaransa na Koriya ta Kudu da kuma na Amurka

Gwamnatin China ta bar duniya tsawon kwanaki, tana jiran samun tabbacin cewa Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un zai ziyarci Beijing, a karon farko a wata kasar waje, inda aka ce ya ce zai yi watsi da shirinsa na kera makaman nukiliya.

To yanzu dai kamfanin dillancin labaran China ya fitar da bayanan wannan ziyara ta farko mai tarihi, ta shugaba Kim Jon-un tun da ya hau mulki shekara bakwai da ta wuce.

An ce a yayin ganawar Shugaba Xi Jinping ya gaya wa takwararn nasa na Koriya ta Arewa China na nan kai da fata ga shirin raba yankin Koriya da makaman kare dangi.

Shi ma a nasa bangaren Kim Jong-un an ce ya amsa da cewa watsi da shirin na mallakar makaman kare dangi matsaya ce da Koriya ta Arewa ta yi amanna da ita.

Ana ganin wadannan kalamai alamu ne na Koriya ta Arewa na neman wata dama da za ta yi watsi da shirin nata na kera makaman kare dangi salun-alun.

Tsohon mai shiga tsakani na Amurka a kan shirin mallakar makaman nukuliya na Koriya ta Arewa Christopher Hill, ya ce wannan ganawa tsakanin shugaban na Koriya ta Arewa da kuma na China tana da matukar muhimmanci.

Ya ce: ''Hukumomin China sun nuna wa Kim Jon-un karara cewa ba za su karbe shi ba har sai ya koma kan turbar aniyar watsi da shirinsa na kera makaman nukuliya.''

Christopher Hill ya ce a yanzu dai China tana da fatan cewa shugaban na Koriya ta Arewa lalle zai gabatar da batun watsi da makaman nukiliyar idan ya gana da Donald Trump.

Ziyarar ta Kim Jong-un a China kamar wata sharar fage ce ga ganawarda zai yi da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in da kuma Shugaba Donald Trump na Amurka

Labarai masu alaka