Za a rataye direba saboda kisan uban gidansa bature a Ghana

'Yan sanda sun kama direban ne bayan kisan ba Amurken Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption 'Yan sanda sun kama direban ne bayan kisan ba Amurken

Wata babbar kotu a birnin Accra na kasar Ghana, ta yanke wa Kofi Seidu, wani direba hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an same shi da laifin kashe wani ba-Amurke dan asalin kasar BIrtaniya Reverend Sydney Barnes.

Direban ya kashe mutumin mai shekaru 70 ne a wata tsohowar gona da ke Nsawam a shekara ta 2010.

Hakan ya faru ne bayan wasu masu taimaka wa alkalai su bakwai sun yanke hukunci game da laifin da ya yi a kan laifin kisan kai.

Kotun ta kuma wanke wasu mutum biyu da ake zargin suna da hannu a kisan.

Ba Amurken dai, ya kafa wata coci mai suna Crossroads Christian Mission a garin Kofridua da ke jihar Gabas, kuma Kofi Seidu shi ne direbansa.

A shekara ta 2010 ne, ya yi tafiya zuwa Amurka yayin da a ranar da zai dawo Ghana, direbansa Kofi Seidu ya dauko shi daga filin jirgin sama, kuma shi ne karshen ganin da aka yi wa Reveren Barnes.

'Yan sanda sun kama direban wanda daga bisani ya fallasa cewar, an hada baki da shi ne a kan ya kashe Reveren Barnes, inda ya yi awon gaba da kudi dala 3,000, kudin da Mr Banes din yazo da su daga Amurka.

Ba kasafai ake yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a Ghana ba.

Labarai masu alaka