Najeriya: An kashe fiye da mutum 60 a Zamfara

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da wani ganau kan kisan Zamfara

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hira da wani ganau mazaunin garin ya yi wa BBC kan harin farko:

Mazauna wani kauye da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun ce barayin shanu sun kashe sama da mutum 60 a kwanaki biyu da suka wuce.

Sun shaida wa BBC cewa mutum 15 aka kashe a harin farko.

Sauran kuma an kashe su ne a wasu jerin hare-hare da barayin suka kai lokacin da ake jana'izar mutanen farko da suka hallaka, inda mutum uku ne kawai suka rayu.

A ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai makon da ya gabata a jihar, ya umarci jami'an tsaro su kawo karshen miyagun laifuka da ake aikatawa a jihar.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya gaya wa BBC cewa a lokacin da suka shiga garin, sun sami gawawwaki uku na mutanen da maharan suka kashe.

Ba a daina kashe mutane ba

Hakkin mallakar hoto zamfara government
Image caption An kashe mutane da dama a sabbin hare-haren jihar Zamfara

An dade ana fama da kashe-kashen mutane a jihar Zamfara, al'amarin da ya addai mazauna yankin.

Sai dai duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi har yanzu lamarin bai sauya ba.

A baya ma wani dan majalisar dattawa da ke wakiltar jihar ya zargi Gwamna Abdul'aziz Yari da cewa ya san masu kai hare-haren, zargin da gwamnatin jihar ta musanta.

A ranar 10 ga watan Maris din nan ma, gwamnatin jihar ta tabbatar da kashe Buharin Daji, wanda shi ne jagoran barayin shanun da suka addabi jihar da hare-hare.

Amma ga dukkan alamu kisan nasa bai sa an daina kashe mutane ba.

Labarai masu alaka