Abin da ya sa matasa suka kafa jam'iyyarsu a Najeriya

Wannan dai shi ne karon farko da aka kafa sabuwar jamiyya ta matasa zalla Nigeria Hakkin mallakar hoto Maryam Laushi
Image caption Wannan dai shi ne karon farko da aka kafa sabuwar jamiyya ta matasa zalla a Nigeria

A baya-baya nan ne hukumar zabe a Najeriya ta bai wa matasa damar kafa jam'iyyar Modern Democratic Party ta matasa zalla.

Wannan dai shi ne karon farko da aka kafa sabuwar jamiyya ta matasa zalla tun bayan da Najeriya ta koma kan tafarkin mulkin dimokradiya shekaru 19 da suka gabata.

Sakatariyar yada labaran jam'iyyar ta MDP, Maryam Laushi ta ce jam'iyyar tasu ba za ta tsayar da wadanda suka tsufa takara ba.

"Idan an zo maganar takara ka da ya zamanto cewa datijjai ne kawai suka cika wuri, wadanda suka tsufa da yawa ba za su iya aikin da ya kamata ba, ba su da irin tunanin da muke bukata," a cewar Maryam.

Sai dai duk da cewa kafuwar jam'iyyar alama ce da ke nuna cewa matasa a kasar kan iya sanya zare da datijjai a zaben 2019 , amma tambayar anan ita ce ko jam'iyyar tasu za ta iya fafatawa da manyan jam'iyyun siyasa biyu da suka fi tagomashi a kasar

Ko da yake matasan sun ce fatansu shi ne jam'iyyar ta samu karbuwa daga wurin jama'a.

Hakkin mallakar hoto Social Media
Image caption Ahmed wani matashi ne da ke son tsayawa takarar shugaban kasa a 2019

"Game da dalilin da yasa bamu shiga manyan jam'iyyun kasar da suka fi tagomashi ba, na farko shi ne ba dole bane saboda akwai wurare da yawa da mutane za su iya tsayawa takara, da ba sa kallo sai shugaban kasa", a cewar Maryam Laushi.

"Muna son idan mu ka yi takara mu ci zabe amma kuma muna son mu sauya yadda mutane suke tunani da kuma yada suke abubuwa."

Ta kuma ce tana son mutane su fahimci cewa ko da a yau ne suka kafa jam'iyya, nan gaba jam'iyyar tasu za ta kara girma.

Da wanne kudi za a tallafa wa MDP?

Game da harkar tara kudi kuwa matasan sun ce asusunsu a bude yake ga duk wanda ke son ya bayar da gudunmuwar komai kankantarta.

"Mun ware wani sashe a shafinmu na intanet inda mutum zai iya bayar da abin da bai fi karfinsa ba," a cewar Maryam Laushi.

Mata a siyasa

Jam'iyyar ta MDP ta ce akwai gibi a yawan matan da ke Majalisar Dokokin Najeriya idan aka kwatanta da maza, amma ta ce daga cikin aniyar MDP ita ce ta gano abubuwan da suke kawo tarnaki ga matan da suka tsaya takara.

A makon da ya gabata ne hukumar zabe ta bai wa matasan lasisin kafa jam'iyyar MDP.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da matasan ke jiran kudurin dokar da majalisa ta aikewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu, domin cire dokar da ta iyakance yawan shekarun masu takara a dokokin zaben kasar.

Sharhi

A iya cewa dai wannan hobbasar da matasa suka fara wani gagarumin aiki ne suka dauko, ganin cewa a kasa irin Najeriya ba a faye bai wa matasa wata dama ta a dama da su ba a harkokin siyasa.

Wasu matasan ma dai da dama ayanzu haka sun fara kokawa kan yadda dattijai a al'umominsu, kamar yadda wani matashi da yake son tsayawa takara a 2019, wanda ba ya so a ambaci sunansa a ya shaida wa BBC.

Ya ce: "Dattijai ba su yarda cewa za mu iya jan ragamar shugabancin ba don haka suna gayawa sauran mutane cewa lallai ba za mu iya ba ka da a zabe mu.

"Ai kuwa wannan ba karamin ci baya ba ne a gare mu."

A yanzu dai a iya cewa sai dai a zuba ido don 'yar manuniya ta nuna abun da zai faru a 2019.

Wacece Maryam Laushi?

  • Shekararta 27
  • 'Yar asalin garin Gombi ce a jihar Adamawa amma a Kaduna ta girma
  • Sune suka fara fafatuka a gangamin "Not young to run".
  • Burinta a kafa Nigeriyar da matasa za su jagoranta
  • An taba ba ta lambar yabo ta SMES100
  • Tayi karatun digri kan tallace-tallace da aikin jarida a Jami'ar Coventry da ke Ingila
  • Tana karatun digiri na biyu kan aikin jarida a Jami'ar Toulouse da ke Faransa

Labarai masu alaka