Sojin Amurka sun hallaka babban dan Al-Qaeda a Libya

Shugaban Al-Qaeda Ayman al-Zawahiri, Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin shi ne na farko na sama da rundunar sojin Amurka a Afirka ta kai kan 'yan Al-Qaeda a yankin kudu-maso-yammacin Libya shekara 2 bayan da ta gama da ISIS a can

Rundunar sojin Amurka da ke Afirka ta ce ta yi nasarar hallaka wani babban kwamandan kungiyar Al-Qaeda , Musa Abu Dawud, a hare-haren sama da ta kai a kudancin Libya a karshen makon da ya gabata.

Ana daukar wannan babban kwamanda Musa Abu Dawud a matsayin mai tsattsauran ra'ayi wanda ke barazana da kuma tsara kai hare-hare a kan muradun kasashen yammacin duniya a yankin Afirka ta Arewa.

A sanarwar da rundunar mai suna AFRICOM a takaice ta fitar, ta ce an tsara kai harin da ya yi sanadiyyar kashe babban jami'in ne da hadin guiwar gwamnatin Libya wadda kasashen duniya suka amince da ita.

A wannan harin sama da sojin na Amurka suka kai ranar Asabar sun yi nasarar hallaka mayakan masu tsattsauran ra'ayi da ke ikirarin Jihadi su biyu a wani sansanin kungiyar ta Al-Qaeda da ke garin Ubari mai dausayi a hamada.

Daya daga cikinsu shi ne Musa Abu Dawud wanda aka yi amanna shi ne ke jagorantar shirin daukar mayaka a yankin.

Yana da dadadden tarihin alaka da tsattsauran ra'ayi a yankin Afirka ta Arewa, tun daga farkon shekarun 1990.

Da farko Musa Abu Dawud dan kungiyar Salafiyya ta Algeria ne da ke da'awa da kuma yaki, wadda daga baya ta rikede zuwa reshen kungiyar Al-Quaeda a yankin Maghreb.

A shekara ta 2016 ne ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ayyana shi a matsayin dan ta'adda na duniya.

Jami'an Amurka sun yi amanna shi ya kitsa miyagun hare-hare da dama da kungiyar ta Al-Qaeda ke kaiwa a yankin, ciki har da wanda aka kai wani sansanin soji a Algeria, da wanda aka kai kan wasu dakarun Tunusia da ke sintiri a tsaunukan Chaambi na kasar.

Ba a san lokacin da wannan babban kwamanda na kungiyar ta Al-Qaeda Musa Abu Dawud ya koma Libya ba.

Ko da yake sai a karshen mako ne aka bayyana kai harin, ya dauki sojin Amurkar kwanaki da dama su tabbatar da mutuwar manyan jami'an na kungiyar, bayan abin da suka kira kammala nazarin illar da harin ya yi.

Shi dai yankin kudancin Libya yawancinsa babu doka da oda, kuma wannan gari na Ubari na karkashin ikon kungiyoyin mayakan sa-kai ne daban-daban.