Shin lambar yabon da aka bai wa Buhari ta 'boge' ce?

Buhari Hakkin mallakar hoto Bashir Ahmed Twitter
Image caption A ranar Litinin ne wasu da aka ce iyalin Martin Luther ne suka ziyarci fadar shugaban Najeriya inda suka ba shi lambar yabon

Cibiyar The King Center, wacce ke adana tarihin fitaccen bakar fatar nan na Amurka, marigayi Martin Luther, ta nesanta kanta daga lambar yabon da aka bai wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Ranar 26 ga watan Maris ne wasu da aka ce iyalin Martin Luther ne suka ziyarci fadar shugaban Najeriya tare da rakiyar mai ba shi shawara kan harkokin 'yan kasar mazauna kasashen waje, Abike Dabiri, inda suka ba shi lambar yabon da ake kira 1st Black History Month National Black Excellence and Exceptional African Leadership Award 2018.

Sun ce an ba shi lambar yabon ne saboda jajircewarsa wurin mulki na gari.

Sai dai a wani sako da cibiyar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar 28 ga watan Maris ta ce "ba cibiyar The King Center ce ta bai wa Shugaba Buhari lambar yabo ba, kuma ba 'ya'yan #MLK da #CorettaScottKing ne suka ba shi ba."

Fadar shugaban kasa ta shaida wa BBC cewa lambar yabon ba ta boge ba ce kamar yadda wasu ke zata.

A cewarta, nan gaba kadan za ta fitar da sanarwa domin yin karin haske kan batun.

Wannan batu dai ya jawo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu ke caccakar shugaban kasar "saboda bai wa kasar kunya a irin karairayin da take yi da zummar boye gazawarta wurin gudanar da mulki".

Wani mai amfani da shafin Twitter Donn Rolly ya rubuta cewa: "Amma mutane mu duba mana. Yaya za a damfari Shugaba Buhari irin haka da lambar yabon boge kamar wacce aka yi a Aba."

Sai dai yayin da 'yan kasar da dama ke kushe tare da ganin baiken gwmnatin Buharin kan wannan lambar yabo, wasu kuwa suna ganin lambar yabon ba ta boge ba ce, inda har suke nuna goyon bayan gwamnatin.

Hakkin mallakar hoto Bashir Ahmed Twitter

Labarai masu alaka