Ko Buhari bai isa ya hana ni fadar gaskiya ba – Dino

senata Dino Melaye ya karyata rundunar ,yan sanda Nijeriya Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/DINO MELAYE
Image caption Rundunar `yan sandan Najeriya ta ayyana Sanata Dino Melaye a cikin mutanen da take nema ruwa-a-jallo

Dan majalisar dattawan Najeriya mai jawo ce-ce-ku-ce, Sanata Dino Melaye ya ce ba zai yi shiru da bakinsa ba matukar ya ga wani abu da ake gudanarwa a gwamnati da bai dace ba.

Sanatan ya shaida wa BBC cewa baya tsoron tsage gaskiya a duk inda ta kama a fade ta, ba kuma ya duba daga jam'iyyar da mutum ya fito indai batun gaskiyar ya kama ko dan jam'iyyar adawa ta PDP ne, ko kuma APC mai mulki.

''Ni ba na tsoron kowa, idan akai abin da ba daidai ba kuma na ga babu gaskiya a ciki sai na fada, ba na jin tsoron kowa indai ina da gaskiya."

"A halin da ake ciki ni fa ko Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ko Bukola Saraki, ko Dogara kai ko uban da ya haife ni idan ya yi ba daidai ba sai na fada, babu wanda ya isa ya hana ni fadar gaskiya sai dai a kashe ni,'' inji Dino Melaye.

Sai dai har yanzu gwamnatin jihar Kogi ba ta mayar da martani ba game da batutuwan da sanatan ya zarge ta a wannan hirar ba, amma a baya ta sha musanta su.

A ranar Laraba ne rundunar `yan sandan kasar ta ayyana dan majalisar dattawan a cikin mutanen da take nema ruwa-a-jallo, bisa tuhumar da wata kotu ke masa ta taimaka wa miyagun ayyuka, zargin da ya musanta.

Haka zalika akwai kalubalen da yake fuskanta na kiranye daga al`ummar mazabarsa.

Karin labaran da za ku so ku karanta

Sai dai ya ce har yanzu mutanensa na kaunarsa don haka zai ci gaba da wakiltarsu har zuwa shekarar 2019.

Har ila yau dan majalisar ya zargi Gwamnan jihar Yahaya Bello da hannu a yunkurin yi masa kiranye.

Tsakanina da Gwamnan jihar Kogi

"Wallahi, wallahi babu wani abu da ya hada ni da Gwamna Yahaya Bello. Ni dai na taba fitowa na ce ya biya ma'aikata albashi," in ji Sanata Dino.

"Yahaya Bello ya yi kusan shekara uku bai hanya ko da ta Kilomita daya ba a jihar Kogi. An kulle makarantun Kogi kusan shekara daya," in ji shi.

Jayya tsakanin majalisa da bangaren zartarwa

Sanatan ya kare majalisar dangane da rashin jituna da ke tsakaninsu da bangaren zartarwa, lamarin da ke haddasa jinkiri wajen aiwatar da ayyukan gwamnati, ciki har da batun kasafin kudin kasar.

Ya ce rashin bayyanar ministoci a gaban kwamitocin majalisar don su kare kasafin kudin ma'aikatansu shi ne dalilin da ya sa aka samu jinkiri wajen amincewa da shi.

  • Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da Sanatan ya yi da Ibrahim Isa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Saurari hirar da BBC ta yi da Sanata Dino Melaye

Dino Melaye a takaice

  • Dan asalin jihar Kogi, amma an haife shi a Kano
  • Shekararsa 44
  • Ya yi karatun firamare a Kano
  • Ya yi digirinsa a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya
  • Yana wakiltar Kogi Ta Yamma a majalisar dattawan Najeriya
  • Ya taba zama dan majalisar waklilan Najeriya har sau biyu
  • An san shi da tarar aradu da ka a harkokin siyasa
  • Ya taba karbar lamar yabo na dan majalisar wakilan da babu kamarsa daga wata kungiyar matasa

Labarai masu alaka