Dole a hukunta wadanda suka wawashe dukiyar Najeriya - Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo Hakkin mallakar hoto AHMED OUOBA/AFP/GETTY IMAGE
Image caption Almundahanar shekara biyar baya ita ta lalata Najeriya in ji mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce dole ne a tuhumi wadanda suka wawashe dukiyar kasar.

Osinbajo ya bayyana hakan ne ranar Alhamis 30 ga watan Maris, a wurin taron gabatar da kasidu na masana karo na goma na girmama tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagora a jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinuba a Ikko.

Ya ce: ''Idan kana yaki da rashawa kamar yadda muke yaki da ita, to rashawa za ta yake ka. Amma kuma mun kudiri aniya ba gudu ba ja da baya.

''Idan ka saurari labarin wadannan matasa, idan ka saurari labarin masu rauni da nakasassu da sauran ire-irensu, mutanen da alhakinsu ya rataya a wuyanmu, wadanda suka zabe mu, to dole ne mu tashi mu kare hakkinsu.

A bisa wannan dalili ne za mu tabbatar da cewa wadanda suka rika debe dukiyar kasar nan sun fuskanci hukunci.''

Mataimakin shugaban na Najeriya ya kara da cewa gwamnatin Buhari tana iya kashe karin kudi saboda a cewarsa, ''idan ba ka saci dukiyar jama'a ba, za ka iya kashe kudi wajen gudanar da ayyukan da suka shafi jama'ar.

Osinbajo ya ce, lokacin da suka fara wannan tafiya a 2014 ta gwamnatinsu, jam'iyyarsu ta APC ta kuduri aniyar sauya yadda ake kallon al'amuran kasar.

Karin labaran da za ku so ku karanta

Ya ce sun lashi takobin sauya yadda ake kallon kasar a matsayin mai arzikin albarkatun kasa da ma mafi yawan arzikin na al'umma, amma kuma a kullum ake bannata wannan arziki ta hanyar gagarumar rashawa ba tare da ana hukunta masu wawure wannan dukiya ta gwamnati ba, sai sun sauya hakan.

Farfesa Osinbajo ya ce game da yakin da suke yi da rashawa, sun gano cewa, kamar yadda Shugaba Buhari ya ce, ''idan ba mu kashe rashawa ba, rashawa za ta kashe mu.

Mataimakin shugaban na Najeriya ya ce daga abin da ya gani a gwamnati a sheakar uku da ta wuce, almundahanar da aka yi a kasar a cikin shekara biyar ta baya, ita ce ta lalata tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce dalilin da ya sa suke magana a kan lamarin shi ne, farko, dole ne su nuna wa jama'a cewa ba za su iya ci gaba da wannan ta'ada ba.

Kuma babu wata kasa a duniya da za ta kyale ana bannata dukiyartsa kamar yadda bannata arzikin Najeriya kuma ta yi tsammanin dorewa da tattalin arzikinta.

Labarai masu alaka