Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da 'yan Afirka a makon jiya.

Bayanan hoto,

Ranar Talata, ranar da aka shiga kwana na biyu na zaben shugaban kasar Masar, wannan matar ta yi rawa a kusa tuta, bayan ta kada kuri'arta a birnin Alkahira...

Bayanan hoto,

Washegari ma an yi wani salon rawar Sufaye a wurin kada kuri'a inda wannan mutumin ya tsaya kusa da fastar Shugaba mai-ci wace a jikinta aka rubuta: "Ku je ku kada kuri'unku"...

Bayanan hoto,

Sai dai an tsaurara tsaro lokacin zaben. Akasarin 'yan takarar jam'iyyun hamayya sun ki shiga zaben, yayin da aka tilasta wa wasu janyewa daga cikinsa.

Bayanan hoto,

Nan kuma mutanen ke murna a wajen babbar kotun da ke Freetown a Saliyo bayan kotun ta bayar da umarni a gudanar da zaben shugaban kasar zagaye na biyu ranar Asabar...

Bayanan hoto,

Masu kada kuri'a na tambayar 'yan takara matakin da za su dauka wurin inganta tattalin arzikin da ke cikin kangi. Wasu mutane, cikinsu har da wannan matar, na daga cikin wadanda suka fi fama da talauci a duniya.

Bayanan hoto,

Ranar Talata, makada da mawakan gargajiya sun baje kolinsu a wurin bikin bankwana da shugaban Botswana Seretse Ian Khamawanda ya sauka daga mulki ranar Asabar...

Bayanan hoto,

... wannan matar na cikin mutanen da suka halarci wurin bikin a garin Serowe, mahaifar shugaban kasar.

Bayanan hoto,

Ranar Laraba, dan siyasa Hassan Ayariga ya hau kan doki inda ya zagaya da shi cikin Accra, babban birnin Ghana, domin bijire wa rahotannin da ke cewa Amurka za ta kafa sansanin sojinta a kasar.

Bayanan hoto,

Ranar Alhamis, kura ta turnuke a Khartoum, babban birnin kasar Sudan abin da ya tilasta wa hukumomi soke sauka da tashin jiragen sama.

Bayanan hoto,

Ranar Juma'a, wannan motar ta yi kaca-kaca bayan wani bam da aka tasa a kan wata hanya mai cike da jama'a a birnin Mogadishu na Somalia, kwana daya kafin lokacin.

Bayanan hoto,

A ranar ce kuma a can Beijing, 'yan makaranta suka yi layi suna jiran isar shugaban kasar Namibia Hage Geingob wanda ke ziyara a China.

Bayanan hoto,

Ranar Laraba, an dauki hoton dan wasan kurket din nan na Australia Steve Smith lokacin da yake fita daga Afirka ta Kudu bayan da ta bayyana cewa ya yi amfani da wata takarda domin lalata kwallo lokacin wasa tsakanin kasashen biyu.

Bayanan hoto,

Ranar Lahadi, an yi wasan karshe na kwallon zari-ruga a kasar Kenya, wanda aka kammala cike da ce-ce-ku-ce.

Bayanan hoto,

Daga karshe, wannan yaron ya buga kwallo a yankin kudancin Sahara na kasar Morocco a bikin duniya na makiyaya.

Pictures from AFP, Reuters, EPA and Getty Images.