Falasdinawa sun yi mummunar zanga-zanga a Gaza, An kama wanda ya 'watsa wa' budurwa Acid

Dino Melaye ya ce ko Buhari bai isa ya hana shi fadar gaskiya ba

Dan majalisar dattawan Najeriya mai jawo ce-ce-ku-ce, Sanata Dino Melaye ya ce ba zai yi shiru da bakinsa ba matukar ya ga wani abu da ake gudanarwa a gwamnati da bai dace ba.

''Ni ba na tsoron kowa, idan akai abin da ba daidai ba kuma na ga babu gaskiya a ciki sai na fada, ba na jin tsoron kowa indai ina da gaskiya," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/DINO MELAYE
Image caption Rundunar `yan sandan Najeriya ta ayyana Sanata Dino Melaye a cikin mutanen da take nema ruwa-a-jallo

An kama wanda ya 'watsa wa' budurwa Acid

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wani wanda ake zargi da watsa wa wata daliba ruwan Acid a garin Maiduguri.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno DSP Edet Okon ya shaida wa BBC cewa rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da masu fashi da makami ne ta kama wanda ake zargin mai suna, Musa Faisal, a jihar Kano ranar Alhamis.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kawo yanzu mutanen da ake zargin ba su ce komai ba kan batun

Falasdinawa sun yi mummunar zanga-zanga a Gaza

Dubban Falasdinawa sun fara zanga-zangar a kan iyakarsu da Isra'ila a ranar farko ta fara zanga-zangar da za su kwashe tsawon kwana shida suna yi.

Ma'aikatar lafiyar yankin Falasdinawa ta ce akalla mutum takwas ne suka mutu yayin da wadansu kimanin 750 suka ji raunuka bayan fara zanga-zangar a ranar Juma'a.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Falasdinawa sun kafa wadansu sansanoni guda biyar a kan iyakarsu da Isra'ila don yin zanga-zangar wanda suka wa lakabi da 'Great March of Return'

Dan wasan Man Utd na son buga wa Najeriya

Dan wasan karamar kungiyar Manchester United Tosin Kehinde ya ce a shirye yake ya taka wa tawagar Najeriya leda.

Kehinde mai shekara 19, wanda yake wasa a karamar kungiyar United 'yan kasa da shekara 23 yana da damar buga wa Najeriya, ko kuma Ingila wasa, amma ya ce shi ya fi son Najeriya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An haifi Kehinde ne a Legas, amma ya tashi ne a Birtaniya

Karanta karin wasu labaran

Kalli bidiyonmu na yau

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda dakarun Isra'ila suka tarwatsa Falasdinawa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ma'aikata na amfani da helkwafta wajen zuwa aiki a Brazil

Domin samun karin bayani da kuma tofa albarkacin bakinku a kan wadannan labaran, sai ku garzaya shafinmu na BBC Hausa Facebook.

Labarai masu alaka