An kama wanda ake zargi da watsa wa budurwa Acid a Maiduguri

'Yan sanda Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wani wanda ake zargi da watsa wa wata daliba ruwan Acid a garin Maiduguri.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno DSP Edet Okon ya shaida wa BBC cewa rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da masu fashi da makami ne ta kama wanda ake zargin mai suna, Musa Faisal, a jihar Kano ranar Alhamis.

Haka zalika rundunar ta ce ta kama wani Muhammad Babangida wanda shi kuma ake zargi da taimaka wa Faisal wajen kai wa budurwar harin.

Kawo yanzu mutanen biyu da ake zargi ba su ce uffan ba game da bayanan da 'yan sandan suka fitar.

Hakazalika babu wata shaida da rundunar 'yan sandan ta gabatar domin tabbatar da wannan zargi, kuma ba ta bayyana lokacin da za ta gurfanar da su a gaban shari'a ba.

Dalibar mai suna Fatima Habu Usman, tana karatu ne a sashen koyon aikin jinya a Jami'ar Maiduguri, kuma ta kasance cikin mayuwacin hali tun bayan harin.

Mutum biyu ne dai ake zargi sun watsa mata ruwan Acid bayan ta shiga Keke Napep ko a daidaita sahu a ranar 16 ga watan Maris.

Dangin dalibar sun shaida wa kafar yada labarai ta PRNigeria cewa, an sace ta ne a gaban wani banki da ta je domin cirar kudi.

Suka ce bayan ta shiga Keke Napep a hanyar Baga ne, ba ta sani ba, sai daya daga cikin mutanen da ke ciki ya fitar da wani kyalle fari ya shafa ma ta a fuska.

Daga nan ne ta fita hayyacinta, kuma sai ta tsinci kanta a kan kwangirin jirgin unguwar Bayan Quarters a Maiduguri misalin karfe daya na rana, kuma an yi ma ta lahani da ruwan guba a jikinta.

Dalibar dai tana shekarar karshe ne a jami'a.

Yanzu haka likitoci na gudanar da gwaje-gwaje a kan Fatima tare da duba yiyuwar ko za a yi mata tiyata a fuska.

Labarai masu alaka