Gwamnan Zamfara ya ce a kashe duk wanda aka gani da bindiga a jihar

Abdul'aziz Yari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamna Abdul'aziz Yari, ya dauki matakin ne sakamakon ci gaba da mummunan kisa da ake zargin barayin shanu na yi wa jama'a a jihar ta Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya, Abdul'aziz Yari, ya umarci jami'an tsaro da su bindige duk wani mutum da suka gani dauke da bindiga a jihar nan take, a zaman hanyar maganin barayin shanu da suka hallaka gomman mutane a jihar a makon nan.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Juma'a a yayin wata hira da manema labarai a garin Mafara bayan wani taron da ya yi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar.

Alhaji Abdul'azizi Yari ya ce, a hare-haren baya-bayan nan da wasu 'yan bindiga suka kai kauyen Bawandaji da ke karamar hukumar Anka da kuma harin da aka kai a karamar hukumar Zurmi, an yi jana'izar mutum 34 sabanin yadda kafafan yada labarai suka bayyana cewa sama da mutane 60 aka kashe.

Gwamnan ya ce, bisa la'akari da irin abubuwan da ke faruwa a wasu kauyuka na jihar, gwamnatinsa ta zauna tare da jami'an tsaro da sauran mahukunta inda aka dauki mataki don ganin irin haka ba ta sake faruwa ba.

Abdul'aziz Yari, ya ce, matakin da aka dauka shi ne, gwamnatin jihar ta bayar da umarnin cewa duk wanda aka kama na rike da bindigar da ake aika-aika da ita, idan soja ko dan sanda ya gan shi, to ba bukatar a bar shi ya sake kwana a doron kasa.

Saboda a cewar gwamnan, wanda aka kaman shi ma ya kashe mutane ba adadi, don haka zamansa a cikin al'umma masifa ne.

Ya ce, an dauki wannan mataki ne bisa la'akari da umarnin Allah (SWT), don haka babu wani da-na-sani a kan wannan mataki.

Kazalika gwamnan ya ce, daga yanzu duk wanda aka kama yana taimaka wa irin wadannan mutane da ke kashe jama'a a jihar da wanda ke karbar kudi kamar na fansa ya kai musu idan sun yi garkuwa da mutane duk hukunci iri daya za a yi musu.

Gwamnan ya ce ba bu wani zancen zuwa kotu idan an kama irin wadannan mutanen, hukunci kawai za a dauka a kansu na kashe su ba tare da bata lokaci ba.

Karin bayani a kan hare-haren jihar Zamfara

Jihar Zamfara na cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar sace-sacen mutane da kisa domin neman kudin fansa.

Sama da mutum 1000 suka rasa rayukansu a cikin hare-haren 'yan fashin a jihar cikin shekaru bakwai.

An dade ana fama da kashe-kashen mutane a jihar Zamfara, al'amarin da ya addai mazauna yankin.

Sai dai duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi har yanzu lamarin bai sauya ba.

A baya ma wani dan majalisar dattawa da ke wakiltar jihar ya zargi Gwamna Abdul'aziz Yari da cewa ya san masu kai hare-haren, zargin da gwamnatin jihar ta musanta.

A ranar 10 ga watan Maris din nan ma, gwamnatin jihar ta tabbatar da kashe Buharin Daji, wanda shi ne jagoran barayin shanun da suka addabi jihar da hare-hare.

Amma ga dukkan alamu kisan nasa bai sa an daina kashe mutane ba.

Labarai masu alaka