Hayakin da jiragen ruwa ke fitarwa na kara dumamar yanayi

Hayakin jiragen ruwa na taimakawa wajen dumamar yanayi a duniya
Bayanan hoto,

Hayakin jiragen ruwa na taimakawa wajen dumamar yanayi a duniya

Fannin safarar jiragen ruwa na duniya na fuskantar karuwar bukatar kara kaimi wajen rage hayaki domin taimakawa wajen magance matsalar sauyin yanayi.

Kwararru sun yi hasashen cewa hayakin da jiragen ruwa ke fitarwa, zai iya samar da kaso akalla daya bisa biyar na hayaki mai haddasa dumamar yanayi nan da shekarar 2050.

Saboda yadda harkar sufurin ta ke a kasashen duniya, fannin sufurin na jirgin ruwa ba a sanya shi a tsare-tsare na kasa wajen rage hayakin da ke haifar da dumamar yanayi.

Gwamnatoci da yawa da suka hada na India da Saudi Arabia, sun kin yarda da ka'idar da ake tsarawa ta hayakin da jiragen ruwa yakamata su rinka fitarwa, inda suke cewa hakan zai iya kawo nakasu ga harkar kasuwanci ta duniya.