'Yan kunar-bakin-wake sun kai hare-hare Maiduguri

Wani wuri da aka kai hari a Maiduguri Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba wanda ya mutu a hare-haren sai wadanda suka kai shi su uku, amma dai wasu mutane sun ji raunuka

An kai wasu hare-haren kunar bakin-wake a yankin Muna Garaj da ke birnin Maiduguri na jihar Borno, ranar Juma'a da almuru, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane da mutuwar maharan uku.

Sai dai rahotanni sun ce ba wanda ya hallaka in banda 'yan kunar bakin-waken guda uku, ko da yake wasu mutane sun samu raunuka.

Ko da yake ba wanda ya dauki alhakin kai harin kawo yanzu, amma wasu na ganin ya yi kama da irin wanda 'yan kungiyar Boko Haram ke yawan kaiwa a wannan wuri.

Tsohon shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, SEMA, shugaban kwamitin da ke kula da ayyukan agaji a jihar ta Borno a yanzu Injiniya Satomi Ahmad ya sheada wa BBC cewa hare-haren an kaisu ne daban-daban har uku.

Ya ce jami'an agaji da na tsaro sun kai dauki ga wadanda suka samu raunuka inda aka tafi da su asibiti.

Jami'in ya ce abin ya faru ne da kusan karfe tara da rabi na dare, ko da yake kafin sannan da wajen misalin karfe bakwai, lokacin sallar Magariba, an rika jin kararraki, wadanda ake gani ko na makaman atilare ne na soji.

Rahotanni sun ce bayan kai harin abubuwa sun lafa, mutane suka ci gaba da gudanar da harkokinsu, kafin zuwa lokacin dokar hana fita ta dare wadda ke aiki daga karfe goma da rabi na dare a birnin, ko da yake yankin da abin ya faru suna da lokacinsu na dokar daban, kasancewar yankin na bayan gari ne.

Wannan dai shi ne karo na kusan 13 da ake kai harin kunar bakin-wake a yankin na Muna Garaj, kuma na biyar a cikin wannan shekarar ta 2018.