Ana zagaye na 2 na zaben shugaban kasar Saliyo

Wata mata na kada kuri'a a zaben Saliyo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutum miliyan uku ne ake sa ran za su kada kuri`a a rumfunan zabe fiye da dubu 11, daga cikin al`ummar kasar sama da miliyan 7

Masu kada kuri'a a Saliyo na zaben sabon shugaban kasar a zabe zagaye na biyu wanda aka daga shi a farkon makon da muke ciki.

Za a yi zaben ne karo na biyu sakamakon rashin samun kuri'un da ya kamata daga wajen 'yan takarar shugabancin kasar su 16 a zaben farko da aka yi.

Jagoran 'yan hamayya Birgediya Julius Maada Bio mai ritaya shi ne ya samu nasara a kan dan takarar shugabancin a karkashin jam'iyya mai mulki, Samura Kamara a zaben da aka yi na farko.

Wakilin BBC a kasar ya ce, wannan shi ne zaben shugaban kasa mafi daukar hankali tun bayan komawar kasar kan tafarkin dimokuradiyya a cikin shekara 22.

An dage zaben ne na karo na biyu wanda a da aka shirya gudanarwa a ranar Talatar da ta wuce, sakamakon umarnin kotu wanda ya biyo bayan karar da aka gabatar ta magudi a zaben farko.

Ana sa ran samun sakamakon zaben a mako na gaba.