An sake kera mutum-mutumin Ronaldo

Asalin hoton, AFP
Ronaldo ya ce ya ji dadi lokacin da aka kaddamar da mutum-mutuminsa bara
Mutumin nan da aka muzanta a shafukan sada zumunta bayan ya kera mutum-mutumin tagulla na dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo bara ya sake kera wani mutum-mutumin dan wasan.
Mutum-mutumin da Emanuel Santos ya kera bara ya sa an rika yi masa shagube da muzantawa inda aka ce mutum-mutumin, wanda aka kaddamar a filin jirgin saman Madeira, bai yi kama da dana wasan ba.
Saidai shekara daya bayan hakan, Mr Santos ya sake tagazawa da zummar rufe bakin masu sukarsa, inda ya kaddamar da sabon mutum-mutumin Ronaldo a shafin intanet na Bleacher Report.
Da yake kare aikin da ya yi, ya ce: "Ni ba mutum ne irin wanda kafafen watsa labarai suka nuna ba; daban nake da yadda suka nuna ni."
A wata hira mai cike da sosai rai da Mr Santos ya yi da Bleacher Report, ya ce muzantawar da aka yi masa baya ya kera mutum-mutumi na farko ta bata ran iyalinsa sannan ya ji tamkar ba a kaunarsa
Mr Santos ya ce ya sake kera mutum-mutumin dan wasan dan kasar Portugal ne ta yadda zai nuna shi cikin "kama da ke nuna tsayin daka."
Mutum-mutumin Cristiano Ronaldo
Ya bayyana cewa kafin ya kera mutum-mutumin na biyu sai da ya rika nuna shakka da jin tosor saboda kada mutane su sake muzanta shi
Asalin hoton, Reuters
Emanuel Santos ya kaddamar da mutum-mutumin Cristiano Ronaldo ne a filin jirgin saman Funchal