Ko shan ruwa da yawa yana da amfani ga fatarka?

Za ka yi tsammanin an yi bincike da dama a kan lamarin, inda aka kasa mutane gida biyu. Hakkin mallakar hoto Getty Images

Maganar cewa fatarka za ta yi kyau idan kana shan ruwa sosai abu ne da ya zama gama-gari amma abin mamakin shi ne babu wata sheda da za ta tabbatar da gaskiyar hakan. Claudia Hammond ta bincika batun.

Idan kana hankoron ganin fatarka tana kyau da sheki kamar matashi a ko da yaushe, da alama a wani lokaci ka taba jin cewa shan ruwa da yawa yana fitar da guba da sauran abubuwan da jiki ba ya so kuma hakan zai sa fatarka ta yi kyau.

To sai dai wani abu shi ne yawan ruwan da ake cewa mutum ya sha ya bambanta daga wuri zuwa wuri, domin a Amurka shawarar ita ce ka sha kofin ruwa takwas a rana, yayin da a wuraren da suke da zafi da yawa ake shawartarka ka sha fiye da haka saboda gumin da kake yi.

To ko ma dai kofi nawa aka ce mutum ya sha, maganar daya ce, shan ruwa da yawa zai sa jikinka ya kasance da wadatar ruwa, wanda zai kasance laimar da za ta hana jikinka bushewa.

Za ka yi mamaki ganin cewa wannan wani abu ne da ya zama ruwan dare amma babu wata sheda da za ta tabbatar da gaskiyarsa.

Za ka yi tsammanin an yi bincike da dama a kan lamarin, inda aka kasa mutane gida biyu.

Kashi daya an sa su , su rika shan ruwa a kai a kai duk tsawon rana, 'yan daya kashin kuwa an sa su sha ruwansu kamar yadda suka saba a rana.

Bayan wata daya ko sama da haka sai kuma a duba bambancin kyawun fatarsu, a tantance ko yawan shan ruwa yana gyara fata.

To a gaskiya da wuya a ce an yi irin wannan bincike, ta wani fannin watakila saboda ruwa abu ne da ba wata doka da za ta takaita ikon amfanin da shi ga wani kamfani, wanda hakan zai sa babu wani kamfani da zai dauki

nauyin irin wannan bincike, inda zai mayar da kudinsa har ma ya samu riba ta hanyar sayar da ruwa idan ya yi karanci.

Binciken da likitan fata Ronni Wolf wanda ke asibitin Kaplan Medical Centre da ke Isra'ila ya yi, ya gano nazari daya ne kawai da aka yi, wanda ya duba tasirin shan ruwa na tsawon lokaci a kan fata. Duk haka ma kuma sakamakon ya kasance mai rudani.

Sakamakon ya kasance ne, bayan sati hudu, rukunin mutanen da suka sha karin ruwa(wanda ba a tace shi da sinadarai ba wato ruwan da ke fitowa daga dutse ko wata kafa ta Allah) fiye da yadda suka saba sha, lemar jikinsu

ta ragu, abin da wasu ke ganin jikinsu ya rike lemar ne, yayin da wadanda suka sha ruwan famfo kuwa, aka ga karin lema a jikinsu.

To amma duk da irin ruwan da kowanne kashi na mutanen ya sha, babu wani bambanci a jikin fatar tasu kan abin da ya shafi santsinta ko kyau.

Wanda hakan ke nuna cewa babu wani tasiri ko illa da rashin ruwa a jikin mutum zai yi wa fata.

Za mu iya auna tasirin hakan ne ta hanyar tsaurin fatar. Hanyar ita ce yawan lokacin da fatar mutum za ta dauka ta koma yadda take daidai, idan aka mintsini mutum aka ja fatar sama.

Idan ba ka da ruwa a jikinka sosai fatarka za ta dan dade kafin ta dawo daidai.

To amma fa ba wai cewa idan shan ruwa kadan abu ne maras kyau ga fata, shansa da yawa kuma a ce yana da amfani ba.

Hakan zai zama kamar a ce tun da rashin cin abinci zai jawo wa mutum cutar yunwa, cin abinci da yawa kuma a ce yana da kyau ba.

Harwayau kamar yadda Wolf ya nuna shi kuma, kamar ace ne tun da mota tana bukatar fetur, hakan na nufin yawan man fetur din da aka zuba mata zai inganta yawan kyawun aikinta.

Wani abin da mutane suka yarda da shi kuma dai shi ne, cewa, idan ka sha ruwa da yawa jikinka zai adana shi.

Amma wai ya danganta da a lokacin da ka sha ruwan, misali, idan ka sha kofin ruwa da yawa a cikin mintina 15 za ka fitsarar da ruwan.

Idan kuma ka sha yawan wannan ruwan a cikin sa'oi biyu jikinka zai rike wannan ruwa.

Akwai binciken da ya nuna cewa shan ruwa mai yawan 500ml yana kara tafiyar jini a hanyoyin da ke cikin fata.

To amma ganin minti 30 bayan haka aka yi nazari, a kan fatar, abin da ba mu sani ba, shi ne ko hakan ya kara hasken fatar.

Wata muhawarar kuma ita ce, kashi 30 cikin dari na abin da fata take dauke da shi ruwa ne, wanda hakan yake sa, ta zama bulbul.

Wannan zai iya zama gaskiya, amma, sabuntar fata ya danganta ne da abubuwan da suka hada da kwayar halitta da zafin ranar da ke samunta da kuma illar shan taba.

To abin da ke daure kai a nan, shi ne, ina maganar cewa shan ruwa kofi takwas a rana yana da amfani, ta samo asali.

Ba tantama, ruwa shi ne sinadari mafi muhimmanci a jiki, wanda idan ba shi za mu mutu cikin 'yan kwanaki, kuma ba shakka akwai karin amfanin da ke tattare da isasshen ruwa a jikin mutum.

A wani bincike da aka yi a 2010 an gano kyakkyawar shedar da ke nuna cewa ruwa yana rage yawan tsakuwar cikin koda a jikin wadanda daman tuni suke da ita.

Amma kuma babu wata sheda mai kwari ta wasu alfanun da aka danganta da ruwan a jiki.

Ana jayayya a kan ka'idar shan kofin ruwa takwas a rana, inda ake ja-in-ja a game da yawan ruwan da ake bukata da zai wanke guba daga cikin koda da kuma ko ruwa yana taimaka wa, ko ba ya taimakawa sha'awar cin abinci ta mutum.

Komai dai ya dangana ne ga yadda yanayin zafi yake, da kuma yadda kake aikata kanka.

Wata al'mara kuma ita ce, yadda ba a ma la'akari da muhimmancin sauran abubuwa na ruwa a jikin.

Ba wai sai abu ya kasance ruwan na zahiri ba, domin ai hatta kayan abinci suna dauke da yawan ruwan da ba ka tsammani.

Yawan ruwan da muke samu a kayan abinci ya dogara ne da inda muke zaune.

A Amurka kashi 22 cikin dari ne, amma a Girka, inda mutane suka fi cin 'ya'yan itace da ganyayyaki abin ya fi haka.

Matsalar dai gaba daya ita ce, rashin wata cikakkiyar sheda ta tabbatar da cewa shan ruwa da yawa yana kawo wani sauyi mai kyau a fatarka.

Ba za mu iya cewa tabbas babu ba, amma dai babu shedar cewa yana yi.

Wanda wannan ya kawar da maganar yawan ruwan da ya kamata ka sha a kullum.

Tun da dai abin ya dogara ne ga yanayin zafi ko sanyi da kuma abin da kake yi, saboda haka akwai kyakkyawan tsari na jikinmu da zai taimaka. Wannan ba komai ba ne illa kishirwa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Is drinking extra water good for your skin?

Labarai masu alaka