Wane ne zai iya hana Tafkin Chadi kafewa?

  • Daga Will Ross
  • BBC News
Lake Chad

Asalin hoton, Getty Images

Tafkin Chadi - cibiyar samun ruwa ga miliyoyin mutane a Afirka ta Yamma - ya kafe da kimanin kashi tara cikin goma saboda sauyin yanayi, da karuwar jama'a da yawan noman rani da ake yi a kusa da shi.

Shin yunkurin da ake yi na ceto shi tun daga shekarun 1980 zai hana shi kafewa?

"Wannan yunkuri ba zai yi tasiri ba, kuma ma zancen kawai ne." Wannan ita ce amsar da akasarin mutanen da suka ji cewa za a sake cika Tafkin ruwa domin ya dawo kamar yadda yake a baya suke bayar wa, lokacin da suka ji cewa za a janyo ruwa daga kogin Congo wanda ke da nisan kilomita 2,400 zuwa Tafkin Chadi.

'Yan Najeriya da ke nuna shakku kan wannan aiki, saboda sun ga gwamnatocin da suka gabata sun kasa aiwatar da aikin, sun ce da alama 'yan siyasar da ke yin wannan yunkuri romon-baka kawai suke yi.

Sai dai ministoci da injiniyoyi, wadanda suka yi taro a Abuja kwanan baya kan yadda za a hana Tafkin kafewa, sun ce za su tabbatar burinsu na hana kafewar Tafkin ya cika.

Tafkin Chadi ya samu koma baya da kimanin kashi 90 cikin 100 tun daga shekarun 1960 saboda sauyin yanayi, da karuwar jama'a da kuma aikin noma rani da ba a tsara shi ba.

Kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru ne suka fi cin moriyar Tafkin, domin kuwa yana sanar wa mutum miliyan 20 zuwa 30 ruwan da suke amfani da shi.

Amma duk shekara zaizayewar kasa na ci gaba da yin illa ga yankunan, lamarin da ya jefa mutanen da ke sana'o'i irinsu kamun kifi da noma da kiwo a yankunan cikin garari.

Majalisar dinkin duniya ta ce mutum 10.7m da ke zaune a yankin Tafkin Chadi na bukatar agaji domin su ci gaba da gudanar da rayuwa yadda ya kamata.

"A baya mukan wuce gonakin masara a kan hanyarmu ta zuwa tafkin kuma akwai kwale-kwale da ke kai-komo a cikinsa, inda ake samun masunta da ke cin kasuwar kifi," in ji Mallam Bale Bura, wanda ya girma a yankin a shekarun 1970 kuma yanzu yana aiki da kungiyar masunta ta yankin Tafkin Chadi.

Yanzu manoman da ke amfani da tafkin ba su da yawa.

Wannan shi ne dalilin da ya sa wakilan da suka yi taro a Abuja suka yanke shawarar sake waiwayar batun ceto tafkin wanda wani kamfanin injiniyoyin Italiya Bonifica Spa ya soma a shekarar 1982.

An kaddamar da wani shiri mai suna Transaqua - wanda zai sa a gina magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2,400 wacce za ta taso daga babban kogin Congo ta ratso ta yankin Chari da ke bakin kogi, sannan ta gangaro cikin Tafkin Chadi.

'Ba a dauki mataki ba'

Shirin ya ba da shawara a duka shekara a kai ruwa mai yawan kyubik mita 100bn zuwa ga madatsan ruwa daban-daban na yankin domin samar da hasken wutar lantarki.

"Na tura daya daga cikin injiniyoyinmu Amurka ya sayo taswirar Afirka ta hakika, wadda sojin saman Amurka suka tsara, wacce ke dauke da bayanai kan lungu da sakon Tafkin," a cewar Marcello Vichi, injiniyan kasar Italiya wanda aka dora wa alhakin gudanar da aikin a farkon 1980.

"Bayan mun kwashe watanni muna nazari kan mu kadai, na shaida wa masu ruwa da tsaki kan batun cewa za mu iya ceto Tafkin daga kafewa."

A cewarsa, an mika kwafe 500 na tsare-tsare kan yadda za a ceto Tafkin daga kafewa ga wakilan gwamnatocin Afirka da hukomomin kudi na duniya a shekarar 1985.

Ya kara da cewa "amma babu wanda ya dauki mataki."

Shekara fiye da 30 bayan hakan, an soma mayar da hankali kan batun, bayan da aka fahimci cewa rikicin da ke faruwa a yankin musamman na kungiyoyin tayar da kayar baya, yana da alaka da kafewar tafkin da kuma kaurar da ake yi daga gare shi.

A shekarar 2014, na hau motar bas inda na je birnin Maiduguri domin zuwa Tafkin Chadi. Akwai motoci masu sulke a gaba da bayana, kuma a gefena na dama wani sojan Najeriya ne a kwance yana kwasar barci.

Mun je Kirenawa, daya daga cikin kauyukan da mayakan Boko Haram suka addaba.

A lokacin da muke tafiya, mun yi karo da yankuna da dama da aka yi watsi da su, inda kuma ga ayyukan ci gaba da dama da gwamnati ta yi watsi da su.

An kona gidaje sannan aka bar mutane cikin kaka-na-ka-yi, inda a gaban idanunsu ake kashe 'yan uwansu.

A duk kauyen da muka je, jama'a na korafin cewa matasa ba su da aikin yi kuma ba su da makoma ta gari.

'Munanan ayyuka'

Wannan halin da matasa ke ciki ne ya bai wa shugabannin Boko Haram damar daukarsu aiki a matsayin mayakan kungiyar.

An rika ba su kudi kadan da yi musu alkawarin samun horo, sannan a ba su bindiga lamarin da ya sa da dama daga cikinsu suka shiga kungiyar.

Tabbas ba kafewar da Tafkin Chadi ke yi ne kadai abin da ke haddasa hare-haren masu tayar da kaya - abubuwa da dama da suka hada da rashin gudanar da mulki na gari sun taka muhimmiyar rawa - amma dai talauci shi ne jigon wadannan matsaloli.

"Na san matasa da dama a kauyenmu da suka rungumi harkar tayar da kayar baya," in ji Mallam Bura.

A lokacin da wakilai suka taru a Abuja domin tattaunawa kan yadda za a fuskanci matsalar kafewar Tafkin Chadi ne aka sace 'yan makarantar mata ta Dapchi sama da 100.

A wurin taron, an amince kamfanonin Bonifica da PowerChina, kamfanin da ya gina madatsan ruwan the Three Gorges dam daga kogin Yangtze, su gudanar da bincike kan yadda za a tunkari matsalar.

Sun bayyana cewa za a kashe kusan $50bn idan ana so Gidauniyar ceto Tafkin Chadi ta soma aiki.

Asalin hoton, Group Bonifica

Bayanan hoto,

Aikin zai ci biliyoyin naira

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Boko Haram ta sace fiye da matan Dapchi 100

Asalin hoton, Getty Images

Ga karin labarai da za ku so karantawa: