Kare ya yi ban kwanan karshe kafin mutuwar mai gidansa

Karen ya zama abokin Mr. Robinson tun bayan mutuwar matarsa
Image caption Karen ya kai ziyara ga Mr. Robinson akan gadon da yake jinya kafin mutuwarsa

Mr. Robinson wadda yake dab da mutuwa ya nemi a kawo karensa domin su yi ganawar karshe sa'o'i kadan kafin kafin ya mutu.

A ranar Alhamis ce jami'an kula da lafiyar sa a asibitin Nenwells a Dundee sun bar karen mai suna Collie kai ziyara ga uban gidansa da ke dab da mutuwa.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Malaman asibitin da su ka nuna jinkai bayan sun amince da karen ya kai ziyara

Iyalan Mr. Robinson sun kai ziyara ga asibitin don nuna godiya ga ma'aikatan asibitin da su ka yi kokarin ganin sun yi abin da zai faranta ma sa akan gadon mutuwarsa.

Hukumar yaki da harbuwa da cututtuka daga dabbobi na bayar da umarni akai dabbobi kai wa ziyara ga asibitoci bisa tsattsauran tsaro.

Ma'aikatan asibitin NHS sun nemi ko za a dauke Mr. Robinson dan shekara saba'in wadda ke fama da irin wata cuta ta fibrosis domin ya cika a gidansa .

To amma iyalan sa sun ce fatar Mr. Robinso itace ya samu damar ganawa da karensa Shep kafin ya bar duniya.. to amma sun ce akwai yiwuwa hakan ba zai samu ba.

Babban abin farin ciki

To amma bayan mintuna ashirin an fada mu su cewa za su iya kawo karen mai suna Shep ya gana da mai gidansa. An kawo karen dab da gadon Mr. Robinson.

Ya yi ban kwana na karshe da karen nasa, wanda yake matukar kauna a rayuwarsa.

A sakon da Ashley Stevens, jikarsa ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce "fatan kakana shi ne ya sadu da karensa ko da sau daya ne" kafin ya bar duniya.

Ms. Stevens ta fada wa BBC cewa kakan nata ya samu karen shekaru takwas da suka gabata, wadda ya zama abokin mu'amalarsa tun bayan da matar Mr. Robinson ta mutu.

Ta kara da cewa ma'aiktan NBH sun yi wani abu na ban mamaki da nuna jinkai bayan amincewa da ziyarar da karen ya kai ga ubangidansa..

"Duk da cewa za ake kallon wannan al'amari ba wani babba abu ba ne, to amma kuma yana da matukar tasiri ga wadanda ba su da lafiya a gadon asibiti."

Labarai masu alaka