Nigeria: Sarakunan Zamfara za su nemi agajin MDD

An kashe kusan mutum 1400 a jihar ta Zamfara cikin shekara biyar. Hakkin mallakar hoto ZAMFARA GOVERNMENT
Image caption An kashe kusan mutum 1400 a jihar ta Zamfara cikin shekara biyar.

A Najeriya, wasu shugabannin al'umma a jihar Zamfara sun ce za su nemi Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afrika wajen kawo karshe matsalar tsaro da ta addabi al'umma a jihar.

Daya daga cikin manyan Sarkaruna a jihar, mai martaba Sarkin Zamfara Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad shi ne ya bayyana haka a hira da ya yi da BBC.

Sarkin wanda aka kashe gomman mutane a masarautarsa ya ce za su yi hakan ne idan matakan da hukumomin jihar suka dauka yanzu suka kasa magance matsalar.

A ranar Jumu'ar da ta gabata ne dai gwamnan jihar ya ce ya ba jami'an tsaro umarnin harbe duk wanda aka gani dauke da bindiga a jihar.

Sai dai wasu masana shari'a sun soki matakin da gwamnan jihar ya dauka inda suka ce ya sabawa dokar kasar.

A kwanakin baya ne wani dan majalisar dattawan da ke wakiltar jihar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa masu satar shanu sun kashe kusan mutum 1400 a jihar ta Zamfara cikin shekara biyar.

Labarai masu alaka