Hotunan abubuwan da suka faru a Najeriya makon jiya

Hakkin mallakar hoto Fadar shugaban Najeriya
Image caption Matar Shugaban Najeriya, Aisha Buhari yayin da jaridar Vanguard ta zabe ta gwarzuwar shekarar 2017, lokacin da wadansu manyan shugabannin kafar yada labaran suka kai mata ziyara a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Litinin...
Hakkin mallakar hoto Fadar shugaban Najeriya
Image caption ...a ranar ce Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin iyalan gidan mai fafutikar kwato 'yancin bakaken fata a Amurka, marigayi Martin Luther King, a fadarsa da ke Abuja. Ziyarar ta janyo ce-ce-ku-ce daga bisani.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Serbia ta doke Najeriya da ci 2-0 a wasan sada zumuntar da suka buga a ranar Talata a kasar Ingila.
Hakkin mallakar hoto Fadar shugaban kasa
Image caption Ranar Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas don yin ziyarar aiki ta kwana biyu da kuma kaddamar da wadansu ayyukan da gwamnatin jihar ta yi...
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption ...a ranar ce kungiyar lauyoyi reshen Lagos ta gudanar da zanga-zanga domin kin amincewa da karin harajin da gwamnatin jihar ta yi kan gidaje da kasa.
Hakkin mallakar hoto Majalisar Wakilai
Image caption Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara tare da Sanata Dino Melaye lokacin da suka kai ziyarar ta'aziyya gidan wani dan majalisar wakilai,Umar Baba Jibril daga jihar Kogi, wanda ya rasu ranar Juma'a a gidansa da ke Abuja.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani mutum yayin da aka gicciye shi don nuna yadda aka yi Yesu Almasiyu a wani bangare na fara bukukuwan Easter a Legas ranar Juma'a.

Ga karin labarai da za ku so karantawa:

Labarai masu alaka