Mutum 28 ne suka mutu a harin Maiduguri

A map showing Maiduguri

Akalla mutane 28 ne suka rasa rayukansu lokacin wani artabu tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da sojojin Najeriya a garin Maiduguri da ke jihar Borno.

Mayaka 18 ne suka kaddamar da wani harin kunar bakin wake a ranar Lahadi, kamar yadda wani jami'in sojin kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya ce sun kai harin ne a wadansu kauyuka biyu da kuma wani sansanin sojoji da ke kusa da birnin Maiduguri.

Jami'an agaji sun ce da dama daga cikin mazauna kauye sun mutu ne yayin da suke kokarin tserewa.

Wannan ne hari mafi muni da aka gani tun bayan fara tattaunawa da kungiyar.

Jami'in sojan, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce maharan ciki har da 'yan kunar bakin wake bakwai, sun isa wurin ne da kafafunsu.

Wani jagoran 'Yan Kato da Gora, Ba'Kura Abba Ali, ya shaida wa AFP cewa maharan sun yi kokarin shiga garin Maiduguri ne.

"Zuwa yanzu an tattara gawawwaki 18 daga kauyukan biyu - Bale Shuwa and Bale Kura," in ji Bello Dambatto, wani jami'in hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar.

Ya ce galibin mutanen sun gamu da ajalinsu ne lokacin da suke kokarin tserewa.

Ba za a iya gane ko duka mutanen 18 da suka mutu mazauna kauye ne ba, ko akwai maharan, ko kuma akwai sojoji a cikin gawawwakin ba.

Har ila yau, harin ya jikkata mutum 68, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

An kai harin ne da misalin karfe 8:50 na daren ranar Lahadi agogon Najeriya, kuma an kwashe kimanin sa'a guda ana artabu, inda mutuanen birnin Maiduguri suka rika jin karar harbe-harbe.

A ranar Juma'ar da ta gabata ma an kai wasu hare-haren kunar bakin-wake a yankin Muna Garaj da ke birnin Maiduguri wanda ya jikkata mutane da mutuwar maharan uku.