Ba mu sa Sanata Mantu ya yi mana magudin zabe ba – PDP

Sanata Ibrahim Mantu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanata Ibrahim Mantu ya ce ya sha bai wa jami'an zabe da na tsaro kudi su sauya sakamakon zabe

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce ba da yawunta ne Sanata Ibrahim Mantu ya rika jirkita sakamakon zabe ba, kuma ta ce ba ta taba umartar wani dan jam'iyyarta ya yi magudin zabe ba.

A makon jiya ne tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, ya ce yana da hannu cikin magudin zabukan da aka yi a baya.

Sai dai a wata sanarwa da Babban Sakataren jam'iyyar Kola Ologbondiyan ya aika wa BBC, jam'iyyar PDP ta nisanta kanta daga kalaman sanatan, inda ta ce batun bai shafi jam'iyyar ba.

Sakataren ya ce Mantu ya yi magana ne game da abubuwan da ya yi bisa radin kansa a zabukan da ya shiga. "Ba mu taba sa wani dan jam'iyyar PDP ya yi magudin zabe ba," in ji shi.

"Mutane suna tsayawa takara a karkashin jam'iyyu yayin zabe. A jam'iyyar PDP muna ba dan takara littafin da ya kunshi dokokin zabe da yadda zai yi yakin neman zabe. Amma babu wurin da za mu umarce shi da ya yi magudin zabe a madadin jam'iyya."

"Idan wani dan takara ya saba wa dokokin zabe, ya yi magudin zabe. Ya yi hakan ne bisa radin kansa amma ba bisa umarnin jam'iyyarmu ba. Idan haka ya faru, ba za a dora wa jam'iyyar laifi ba," in ji sakataren.

Sanata Mantu, wanda toshon dan majalisar dattawan ne, fitaccen dan jam'iyyar PDP wanda a lokuta da dama aka zarge shi da hannu wajen cuwa-cuwar siyasa, ciki har da zargin yunkurin sauya kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda zai bai wa tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo damar yin ta-zarce a karo na uku.

Sai dai shi da Cif Obasanjo sun sha musanta zargin.

Mantu ya kasance dan majalisar dattawa daga jihar Filato karkarshin jam'iyyar PDP tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, inda ya fadi zabe.