Gaza: Turkiyya ta yi wa Isra'ila raddi kan Falasdinawa

Protesters hold hands and run

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Juma'a ne Falasdinawa suka fara zanga-zanga a kan iyakarsu da Isra'ila

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun fara yakin cacar baka game da mummunar zanga-zangar da Falasdinawa suke yi yankin zirin Gaza.

Akalla Falasdinawa 16 ne suka rasa rayukansu a ranar Juma'a, bayan da sojojin Isra'ila suka bude wuta kan Falasdinawa masu zanga-zanga.

Shugaba Erdogan ya bayyana Mista Netanyahu a matsayin "dan ta'adda" a ranar Lahadi.

Wannan yana zuwa ne jim kadan bayan da Shugaba Netanyahu ya zargi Turkiyya da kashe wadansu fararen hula da ke kasarta.

Netanyahu ya taba bayyana Erdogan da "mutumin da yake jefa bama-bamai a kauyukan Kurdawa" wato yana nuni da abin da ya faru a yankin Afrin na kasar Syria.

Mista Erdogan ya bayyana martanin Isra'ila kan masu zanga-zangar da "rashin imani."

"Kai Netanyahu! Kai dan kama wuri zauna ne. Kuma kai dan kama wuri zauna ne a wadannan yankuna. A lokaci guda kuma kai dan ta'adda ne," in ji Erdogan a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin ranar Lahadi.

Yakin cacar bakar yana zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila take ci gaba da shan suka kan yadda take amfani da sojoji kan masu zanga-zangar.

Isra'ila ta rika amfani da sojoji wajen dakile zanga-zangar da Falasdinawa suka fara yi a kan iyakarta, wanda za su kwashe tsawon kwana shida suna yi kuma suka yi wa lakabi da "Great March of Return".

Majalisar Dinkin Duniya ta ce daruruwan mutane ne suka jikkata, tun bayan fara zanga-zangar a ranar Juma'a.

Har ila yau, Isra'ila ta yi watsi da kiraye-kirayen da wadansu shugabannin kasashen duniya suke yi na kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa game tashin hankalin.

Zanga-zangar tana zuwa ne gabanin bikin cika shekara 70 da kafa kasar Isra'ila - abin da Falasdinawa suka wa lakabi da "Nakba".