Tsohuwar matar Mandela, Winnie, ta rasu

Winnie Mandela
Bayanan hoto,

Marigayi Mandela ya rabu da Winnie ne a shekarar 1996

Tsohuwar matar marigayi Nelson Mandela, Winnie, ta rasu tana da shekara 81 a duniya.

Winnie Madikizela Mandela ta kasance mai yaki da nuna wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu.

Marigayiyar tana daga cikin mutanen da suka yi wa tsohon Shugaba Mandela rakiya yayin da aka sallame shi daga gidan yari - bayan ya kwashe fiye da shekara 27 yana tsare.

Mai magana da yawun iyalanta Victor Dlamini ya ce: "Ta rasu ne bayan ta yi fama fa doguwar jinya a safiyar ranar Litinin."

An haifi marigayiyar ne a shekarar 1936 a lardin Eastern Cape wanda a da ake kira Transkei.

Ta fara haduwa ne da Mandela a shekarun 1950 kuma sun kwashe shekara 38 a matsayin ma'aurata - kodayake kimanin shekara 30 ba sa tare da juna saboda Mandela yana gidan yari.

Duk da cewa aurensu ya mutu a shekarar 1996, Winnie ta ci gaba da amfani da sunan Mandela da kuma hulda da shi.

'Uwar kasa'

Bayanan hoto,

Winnie Madikizela-Mandela a gaban kotun da ta daure mijinta na tsawon rai da rai

Bayan da aka tsare Mista Mandela, Mrs Madikizela-Mandela ta karbi ragamar fafutukar kwato 'yancin bakaken fatar Afirka ta Kudu.

Ita ma an sha daureta saboda wannan gwagwarmayar da ta yi na neman kafa adalci.

Ga magoya bayanta, ta kasance 'Uwar Kasa' saboda soyayyar da suke da ita a gareta.

Me yasa ta kasance mai raba kawunan jama'a?

Misis Madikizela-Mandela ta kasance mai raba kawunanan al'umma na tsawon gomman shekaru.

An tuhume ta da gudanar da wani bakin mulkin a yankunan birnin Soweto. Wasu mambobin ANC sun raba gari da ita bayan da ta amince da a rika kona wadanda basu goyin bayan fafutukar da ta ke jagoranta ba.

An kuma same ta da laifin yin garkuwa da kuma kashe wani yaro mai shekara 14, Stompie Seipei.

Misis Madikizela-Mandela ta sha musanta tuhumar.

Bayanan hoto,

Misis Madikizela-Mandela (a 1988) ta zama babar alamar nuna turjiya ga mulkin wariyr al'umma na kashin kanta.

Mista Mandela ya goyi bayanta a lokacin da take fuskantar tuhume-tuhumen.

Amma shekaru biyu bayan an sake shi daga kurkuku, aurensu ya mutu. Ma'auratan sun rabu a 1996, amma ta cigaba da amfani da sunansa har bayan mutuwarsa.