Abdul Fattah al-Sisi ya sake lashe zaben Masar

An election poster for President Sisi

Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya sake lashe zaben kasar, inda ya samu kaso 97 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kamar yadda hukumar zabne kasar ta bayyana.

Moussa Mostafa Moussa ne na jam'iyyar al-Ghad ya fafata da shugaban.

Sai dai kaso 41 cikin 100 na mutanen da suka cancanci kada kuri'a ne kawai suka fito lokacin zaben.

Shugaban ya samu adadin kuri'u daidai da wadanda ya samu a zaben shekarar 2014. Amma a wancan lokacin an fi samu fitowar masu kada kuri'a yayin zaben.

Mutane da dama suna ganin zaben na je ka na yi ka ne, saboda yadda mutum daya tilo ne ya kalubalance shugaban kuma a baya ya taba mara wa bukatar ci gaba da mulkinsa baya.

'Yan adawa sun yi kira da kauracewa zaben bayan mutane da dama sun janye daga takara, yayin da aka kama wadansu.

Shugaban ya musanta cewa shi ya tilasta musu janyewa daga zaben.

Shugaba al Sisi ya hanbarar da zababbiyar gwamnatin Mohammed Morsi ne a shekarar 2013 bayan an fara mata zanga-zanga adawa.

Gwamnatin al Sisi ta rika yin dirar mikiya a kan duk wani da ke adawa da ita, yayin da ta daure dubban mutane.

Tun daga lokacin ne kungiyar kare hakkin dan Adam suke bayyana shi a matsayin mai mulkin kama karya.