Hotunan yadda aka yi bikin Easter a fadin duniya

Hotunan yadda mabiya addinin Kirista suka yi bikin Easter a sassan duniya daban-daban.

Bayanan hoto,

Fafaroma Francis lokacin da ya jagoranci taron addu'o'i a gaban fadarsa da ke Vatican ranar Lahadi

Bayanan hoto,

Wadansu dogarawa a gaban cocin St Peter Basilica yayin da ake jiran isowar Fafaroma ranar Lahadi

Bayanan hoto,

Wadansu Kiristoci 'yan Pakistan lokacin da suka halarci taron addu'o'in Easter a birnin Lahore

Bayanan hoto,

Wadansu Kiristoci 'yan Indiya lokacin da suke nuna wadansu kwayaye a wani bangare na bikin Easter a Bangalore

Bayanan hoto,

Wani mutum yayin da aka gicciye shi don nuna yadda aka yi Yesu Almasiyu a Legas ranar Juma'a

Bayanan hoto,

Ana yin hakan ne a wani bangare na fara bukukuwan Easter ranar Juma'a

Bayanan hoto,

Wadansu Kiristoci 'yan darikar Katolika suna addu'o'in Easter a kauyen Ragotna na kasar Belarus

Bayanan hoto,

Fafaroma Francis lokacin da ya jagoranci addu'o'in Easter a fadarsa da ke Vatican

Bayanan hoto,

Fafaroman yayin da yake yi wa wani batisma a fadarsa da ke Vatican ranar Asabar

Bayanan hoto,

Wadansu yara suna yin wasanni a garin Torrance da ke jihar California na kasar Amurka