An kashe mutum 15 a Maiduguri, PDP ta ce ba ta taba sa Mantu ya yi magudin zabe ba

An kashe mutum 15 a Maiduguri

Akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu lokacin wani artabu tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da sojojin Najeriya a garin Maiduguri da ke jihar Borno.

Mayaka 18 ne suka kaddamar da wani harin kunar bakin wake a ranar Lahadi, kamar yadda wani jami'in sojin kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

PDP ta ce ba ta taba sa Mantu ya yi magudin zabe ba

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce ba da yawunta ne Sanata Ibrahim Mantu ya rika jirkita sakamakon zabe ba, kuma ta ce ba ta taba umartar wani dan jam'iyyarta ya yi magudin zabe ba.

A makon jiya ne tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, ya ce yana da hannu cikin magudin zabukan da aka yi a baya.

Sai dai a wata sanarwa da Babban Sakataren jam'iyyar Kola Ologbondiyan ya aika wa BBC, jam'iyyar PDP ta nisanta kanta daga kalaman sanatan, inda ta ce batun bai shafi jam'iyyar ba.

Hakkin mallakar hoto TWITTER/ CHANNELS TV
Image caption Sanata Ibrahim Mantu ya ce ya sha bai wa jami'an zabe da na tsaro kudi su sauya sakamakon zabe

Turkiyya ta yi wa Isra'ila raddi kan Falasdinawa

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun fara yakin cacar baka game da mummunar zanga-zangar da Falasdinawa suke yi yankin zirin Gaza.

Akalla Falasdinawa 16 ne suka rasa rayukansu a ranar Juma'a, bayan da sojojin Isra'ila suka bude wuta kan Falasdinawa masu zanga-zanga.

Shugaba Erdogan ya bayyana Mista Netanyahu a matsayin "dan ta'adda" a ranar Lahadi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Falasdinawa sun kafa wadansu sansanoni guda biyar a kan iyakarsu da Isra'ila don yin zanga-zangar wanda suka wa lakabi da 'Great March of Return'

Tsohuwar matar Mandela, Winnie, ta rasu

Tsohuwar matar marigayi Nelson Mandel, Winnie, ta rasu tana da shekara 81 a duniya.

Winnie Madikizela Mandela ta kasance mai yaki da nuna wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marigayi Mandela ya rabu da Winnie ne a shekarar 1996

Hotunan yadda aka yi bikin Easter a fadin duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fafaroma Francis lokacin da ya jagoranci taron addu'o'i a gaban fadarsa da ke Vatican ranar Lahadi
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fafaroma Francis lokacin da ya jagoranci addu'o'in Easter a fadarsa da ke Vatican
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yin hakan ne a wani bangare na fara bukukuwan Easter ranar Juma'a

Abdul Fattah al-Sisi ya sake lashe zaben Masar

Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya sake lashe zaben kasar, inda ya samu kaso 97 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kamar yadda hukumar zabne kasar ta bayyana.

Moussa Mostafa Moussa ne na jam'iyyar al-Ghad ya fafata da shugaban.

Sai dai kaso 41 cikin 100 na mutanen da suka cancanci kada kuri'a ne kawai suka fito lokacin zaben.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shin Madrid za ta iya sake doke Juventus?

A gobe Talata ne Juventus za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan gab da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai.

A bara dai Madrid ce ta doke kungiyar a wasan karshe na gasar, abin da ya ba ta damar daukar kofin gasar a birnin Cardiff na kasar Birtaniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Madrid ce ta doke Juventus da ci 4-1 a wasan karshe na gasar zakarun Turai na bara

Karanta karin wasu labaran

Domin samun karin bayani da kuma tofa albarkacin bakinku a kan wadannan labaran, sai ku garzaya shafinmu na BBC Hausa Facebook.

Labarai masu alaka