Winnie Mandela: Rayuwar jagorar yaki da wariyar launin fata
Ku kalli hotunan rayuwar jagorar yaki da wariyar launin fata, Winnie Mandela wadda ta mutu tana da shekara 81.

Winnie Mandela: Ga magoya bayanta, ta kasance 'Uwar Kasa'.
Asalin hoton, AFP
Ta shafe fiye da shekara 30 tana gwagwarmaya tare da marigayi Nelson Mandela.
Asalin hoton, Reuters
An sha tsare ta a sanadiyyar wannan gwagwarmayar a karkashin gwamnatin wariyar al'umma.
Asalin hoton, Reuters
Ta gana da shugabannin duniya - kamar Sanata Edward Kennedy na Amurka domin a sako mijinta daga kurkuku.
Asalin hoton, Reuters
An tuhume ta da hannu wajen kashe Stompie Seipei , mai shekara 14 d haihuwa, amma ta musanta tuhumar.
Asalin hoton, PA
Aurenta da Nelson Mandela ya mutu a 1996 bayan da aka sako shi daga kurkuku.
Asalin hoton, Reuters
Winnie Mandela ta zama babbar jami'a a jam'iyyar ANC bayan da ta karbi mulki.
Asalin hoton, Getty Images
Ta cigaba da taka rawa a siyasar kasar - har bayan saukar Mista Mandela daga mulki - a nana tana nuna goyon bayanta ga 'yar wasan motsa jiki Caster Semenya ne.
Asalin hoton, Getty Images
Winnie Mandela a wani taron gangami